Rubutun batsa na iya haifar da yawaitar aikata fyaɗe – Rahama Sabo Usman

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gamayyar Ƙungiyoyin Marubutan Jihar Kano, wato GAMJIK, ƙungiya ce da marubutan adabi suka kafa domin ƙarfafa haɗin kai a tsakanin su da samar da tsari wajen fitar da labaran hikayoyi masu inganci da suka dace da tarbiyyar addinin Musulunci da al’adun al’ummar Arewa. Wani gangami da ƙungiyar ta runguma kuma take neman goyon bayan hukumomi, gwamnati da marubutan adabi a kansa shi ne yaƙi da yaɗuwar rubutun batsa da ya ke neman mamaye harkar rubutun adabi a halin yanzu, matsalar da ƙungiyar GAMJIK ke ganin tana buƙatar a yi mata rubdugu, don a kawo ƙarshen ta baki ɗaya. A yayin taron ƙungiyar na farko da aka gudanar a birnin Kano, wanda ya samu halartar manyan marubuta, manazarta da ’yan jarida, wakilin jaridar Blueprint Manhaja ABBA ABUBAKAR YAKUBU, ya gana da Sakatariyar Ƙungiyar, Rahama Sabo Usman, game da manufofin ƙungiyar da nasarorin da ta ke samu kawo yanzu.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki.

RAHAMA: Sunana Rahama Sabo Usman, ni marubuciya ce, ɗaliba, kuma mai kishin cigaban harkokin adabi.

Ko za ki gaya mana dalilin da ya sa aka kafa wannan ƙungiya?B

abban dalilin da ya sa muka buɗe wannan ƙungiya shi ne domin samar da haɗin gwiwa a tsakanin marubuta, musamman marubutan yanar gizo wato na online, saboda wasu rubuce-rubucen batsa da suka fara yin yawa, wanda wasu marubuta da ba mu amince da tsarin su ba suke yi. Kuma muna ganin suna yin haka ne saboda sun ga babu wani mataki da za a ɗauka a kansu, don babu wata tsayayyiyar ƙungiya ta marubutan online da za ta ɗauki mataki a kansu.

Mutane nawa ne suka ba da gudunmawa wajen kafuwar wannan ƙungiya?

Da farko dai mu biyu ne muka fara tattauna yadda za a kafa wannan ƙungiya, ni Rahama Sabo Usman da Maijidda Adam Suleiman. Sai daga baya kuma wasu maza biyu suka shigo tafiyar, Mubarak Idris Abubakar da Mukhtar Musa Ƙarami. To, daga nan ne tsarin kafuwar ƙungiyar ya fara ƙarfi. Wannan ya gayyato wancan, wancan ya gayyato wannan. Da haka ƙungiyar ta fara ƙarfi har ta kai ga yanzu kusan shugabanni kawai muna da mutum 35.

Waɗanne hanyoyi ku ke bi don ganin kun samu haɗin kan dukkan sauran marubuta?

Har yanzu muna cigaba da tuntuɓa da kira ga sauran marubuta, da su zo mu haɗa kai don ganin mun haɗa ƙarfi da ƙarfe a kai ga cimma manufofin kafa wannan ƙungiya. Don an ce hannu ɗaya ba ya tafi, kuma bishiya ɗaya ba ta daji. Dole sai mun haɗu mun yi ƙarfi sannan za mu iya samun nasara akan wannan aiki da muka ɗauko. Idan har ƙungiyoyin marubuta na nan Kano da na sauran jihohi muka haɗa kai muka yi ƙarfi to, babu wani marubuci da zai fito ya ja da matsayar da ƙungiya za ta yi, ba a kan rubutun batsa kaɗai ba, har ma da sauran wasu matsalolin da muke cin karo da su a harkar rubutun adabi.

Wanne ƙalubale ku ke fuskanta daga su waɗannan marubuta da ku ke kira da marubutan batsa?

Muna fuskantar babban ƙalubale daga irin rubuce-rubucen da suke yi, saboda yadda suke ɓata mana suna. Ana yi wa duk wani marubucin yanar gizo kallon lalatacce ko mai lalata tarbiyya. Shi ya sa ma sauran marubutan adabi suke bata baya da mu, suna ganin mu marasa kunya, marasa ladabi. Kuma abin da ya sa ake yi mana ganin hakan don ba mu iya fitowa mun tsawatar ko mun yaƙi abin da gaske duniya ta shaida ba, shi ya sa ake kallon kamar duk halin mu ɗaya. Wannan zai sa sauran jama’a da masu karatu su fahimci bambancin mu da su, sannan su amince da ƙoƙarin da muke yi.

Wanne ƙoƙari ku ka yi na ganin kun jawo waɗannan marubuta jiki, kun yi musu nasiha da nuna musu irin kuskuren da suke yi, don su canja salon rubutun da suke yi, ba tare da an kai ga fito na fito ba?

Mun yi ta ƙoƙarin fahimtar da su illar abin da suke yi ta cikin guruf-guruf da muke yi a yanar gizo, musamman ma an buɗe wani guruf da aka sa wa suna yaƙi da rubutun batsa, inda ake tattaunawa, amma a ƙarshe da faɗa ake tashi da maganganu marasa daɗi, saboda yadda suke ganin ba mu isa mu hana su abin da suke yi ba. Wani lokaci har da zage-zage da barazanar ɓata suna. Shi ya sa muka fito musu ta nan, inda muke ganin idan hukuma ta shigo ciki, ba su isa su ja da ita ba.

Ta wacce hanya ku ke ganin hukuma za ta shigo ciki?

Dama matakin farko ta isa ga gwamnati shi ne ta hanyar kafa ƙungiya, yanzu Allah ya taimake mu mun yi nasara a wannan ɓangaren. Mune ƙungiyar marubutan online ta farko mai rijista da gwamnati. Sannan mun ziyarci hukumar Hisba ta Jihar Kano don bayyana mata damuwar mu da kuma buƙatar sa bakin su a wannan yaƙi da muka ɗaura da yaɗuwar rubutun batsa.

Wanne irin goyon baya ku ke nema daga ɓangaren Hukumar Kula da Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano da sauran hukumomin gwamnati?

Dama wannan aikin na gwamnati ne, su ne ya kamata su samar da dokoki na yaƙi da waɗannan abubuwan, mu namu mara musu baya ne kawai. Don haka muna kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa, musamman Majalisar Dokoki ta Jihar Kano su tashi tsaye don ganin an samar da dokokin da za su hukunta masu yaɗa rubuce-rubucen batsa.

Kamar yadda aka kafa dokar hukunta masu fyaɗe, domin muna ganin yaɗuwar rubutun batsa a tsakanin jama’a na iya haifar da cigaba da yawaitar aikata fyaɗe. Saboda idan aka yi la’akari da yadda akasarin masu karatun littattafan nan matasa ne masu ƙuruciya, kenan lallai akwai abin dubawa ga gwamnati da masu ruwa da tsaki a ɓangaren rubutun adabi.

Akwai labarin da muka ji na cewa wata yarinya matashiya tana karanta irin waɗannan labarai na batsa daga wayar babarta, a dalilin haka abin ya kai ta ga biya wa kanta buƙata a voye ba da sanin iyayen ba.

Wanne jan hankali za ki yi ga sauran marubuta da ba su shigo cikin wannan Gamayya ta ku ba, da su zo su haɗa kai da ku, don a gudu tare a tsira tare?

Wannan yunƙuri ba namu ne kaɗai ba, duk wani marubuci da ya ke Jihar Kano yana da hakkin shigowa ƙarƙashin wannan Gamayya, don mu yi wannan jihadi na tsarkake rubutun adabi tare da su. Mu kuma a shirye muke mu haɗa kai, mu ba su dama, mu yi aiki tare don cimma wannan aiki na alheri da muka sako a gaba. Muna son kowanne marubuci ya shigo ya ba da tasa gudunmawar.

Yaya ku ke ganin za ku samu nasarar wannan yunƙuri naku, ba tare da shigar da sauran ƙungiyoyin marubuta na sauran jihohi ba?

Kamar yadda na faɗa a baya, wannan aiki ba zai yi nasara ba, ba tare da sa hannun ƙungiyoyi na sauran jihohi ba, musamman kasancewar rubuce-rubuce ne ake yi a yanar gizo, inda kowa ma zai iya yin rubutun batsa, kuma daga kowacce jiha. Dole ne sai marubuta na sauran jihohi su ma sun zo sun haɗa da kai da mu, ta yadda nan gaba yaqin zai tashi daga Jihar Kano ya koma na Arewa ko Nijeriya baki ɗaya.

Wacce karin magana ki ke yawan tunawa a harkokin ki na rubutu?

Rubutunka Kamanninka.

Na gode.

Nima na gode.