Kotu ta tasa ƙeyar matashin da ya yi sanadiyyar rasa ƙafar matashiya Fatima a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Wata kotun majistare dake a Sakkwato ta tasa ƙeyar Aliyu Sanusi Umar matashin da ake zargi da yin tuƙin ganganci da ya yi sanadiyar rasa ƙafar ɗalibar makarantar Khalifa dake Sokoto Fatima.

Wannan dai ya biyo ne bayan ƙarar da lauyan Fatima suka shigar a gaban kotu, da suke buƙatar kotun ta ƙwato wa Fatima haƙƙinta daga wanda ake zargi da zama sillar rasa ƙafarta.

Mahaifin Fatima bayan fitowa daga kotu

Lauyan mai ƙarar a zaman kotun na ranar Litinin ya buƙaci kotun da ta duba yuwar bada belin wanda ake zargin la’akari da tanadin sashe 157 da 161, na dokar jihar Sakkwato na 2019 ta hanyar bada belin wanda ake zargin har zuwa ƙarshen Shari’a.

Sai dai bayan jin bahasin lauya mai shigar da ƙara da wanda ake ƙarar, alƙalin kotun ta bayar da umarnin tasa ƙeyar matashin zuwa gidan gyaran hali har zuwa 29 ga watan Agusta domin cigaba da sauraron shari’ar.

Barista Mansur Aliyu shi ne lauyan wacce ke ƙarar, ya shaida wa wakilinmu cewa, sun shigar da ƙarar ne domin nema wa Fatima haƙƙinta daga wanda ake zargin.

Lauyan da ke kare Fatima

“An shigar da ƙarar ne bisa laifukan yin tuƙin ganganci, da ma tuƙi ba tare da lasisin tuƙi ba, to da aka shigar da ƙarar an bada shi beli a lokacin saboda wata ƙil yana da gata ko shi ɗan manya ne, amma da ƙoƙarin Cif Majistare na babbar kotu, da sashen shari’a na hukumar CID, an tuhume shi da laifuka, kuma mun ji daɗin da kotu ta kai shi gidan yari,” inji lauyan.

Duk ƙoƙarin da muka yi domin jin ta bakin lauyan dake kare wanda ake ƙarar kan lamari yaci tura.