Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Aunty Ayshat Ina jin daɗin karanta littafinki, dan Allah ni ko matsalata a kullum idan na yi wanka, na shirya, in mijina ya dawo, sai ya ce, akwai iya wanka, amma babu gashi, babu hasken fata. Dan Allah aunty ko da akwai abinda za ki bani shawara akai. Please ki taimaka mani. A huta lafiya. Na gode.

AMSA: Wa’alaiki salam warahmatullah. Da farko zan fara da bayyana miki bambancin biyayya ga miji da kuma biye wa miji kan wasu buƙatu na ra’ayin kansa.

Duk da cewa addini ya ce, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki faranta masa, ki biya masa buƙatunsu, hakan ba yana nufin za ki bi shi kamar raƙumi da akala ba. Kuma ba hakan na nufin duk abinda yake so ki yi masa ba tare da la’akari da matsayin sa ga lafiya ko addini ba.

Duk mutumin da ba zai iya amsar kamani da irin surar jikin da Allah Ya yi wa abokin zamansa ba to wannan bai cancanci faɗawa halaka don biyan buƙatarsa ba.

Idan na fahimce ki, kamar mijinki na son matarsa ta yi haske ko na ƙarfin tuwo ne. Me hakan ke nufi? Ki samu hanyar da za ta haskaka mi ki fatarki ko da kuwa mai iya cutar da ke a gaba ce. Dalilin faɗar haka kuwa, yawan maimaita maganar da yake yi.

‘Yar’uwa ki sani, hasken fata dai kala biyu ne. Na farko ba shi da illa ga lafiya da kuma addini. Na biyu kuwa, addini ya haramta kuma yana da babbar illa ga fatar wanda ba za ki gane ba sai nan gaba idan shekaru sun ja.

Na farko shine, amfani da kyawawan mayuka da sabulai da fata ke buƙata. Domin amfani da sabulu ko mai da fata bata aminta da shi ba na kawo matsaloli da dama, ciki kuwa har da duhun fata. Akwai kuma hutu da cin wasu daga cikin cimar da Allah Ya hallita wa bayinSa. A nan kuwa za su taimaka ne kawai wurin bayyana haƙiƙanin hasken fatarki, ba tare da sun kai ga wadda ta ke a ɓoye ba.

Samun sanin ababen da fatarki ke buƙata kuwa mai sauƙi ne, domin ko a bibiyar shafin kwalliya na wannan jaridar za ki iya samun biyan buƙata. Haka ma ta vangaren gashi, akwai matsaloli da yawa da ke hana gashi fitowa ko suke sanya shi zubewa, su ma dai za ki iya samun sanin yadda za ki gyara gashinki cikin sauƙin kuɗi, kamar yadda a kwanakin baya shafin kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja ta wallafa, kuma zamani ne da ilimi yake da sauƙin samuwa, ko ta kafafen sada zumunta za ki mallaki bayyanan da za su gamsar da ke.

Sai ɓangare na biyu, wanda na fi hasashen shine buƙatar mijin na ki, wato sanya fatarki haske ta ƙarfi, wato bilicin. A nan zan iya cewa, ba zai zama abin mamaki ba idan kika biye wa mijinki ba, saboda mata da yawa sun bi wannan tafarkin, amma Ina mai tabbatar mi ki ƙarshen labarinsu bai yi kyau ba.

A wasu ‘yan watanni baya, shafin kwalliya na wannan jarida ya tattauna da wani likita kan sha’anin canza fata, wato bilicin, ya yi bayyanin yadda mayukan ke aikin da ke samar da biyan buƙata ko da kuwa ga baƙar mace, sai dai irin illar da yake yi kafin ya samu nasara babba ce, domin yana karya garkuwar fata, ya barta ba tsaro, wanda hakan zai iya sa mai amfani da su tsufa da wuri da kuma lalacewar fata da wani sa’in ta ke zama abin ƙazanta.

Tambayar da za ki yi wa kanki, shin mijinki zai iya zama da ke ba tare da wulaƙantawa ba idan hakan ta kasance ga fatar da kika lalata don yi masa kwalliya? Yanzu fa fatarki lafiya ƙalau ta ke, haske ne kawai ba ki da, amma ya dame ki da gori, to ina ga ta zama kwandem.

Ki sani, duk namijin da ba ya sonki a yadda kike ko kaɗan bai cancanci ki saka kanki a mawuyacin hali don biyan buƙatarsa ba.

Shawarata, ki rufe kunne da zuciyarki daga damuwa da habaicinsa. Ki nemi hanyar da za ki inganta fatarki ta zama abin sha’awa, amma zancen canza mata launi ki nisanta kanki da shi, ko da kuwa ya furta buƙatar hakan. Ki dinga tuna wa kanki makomarki idan kin aikata, wanda ke kawai ta shafa. Idan kika ga aurenki ya mutu ta wannan sanadi to dama lokacin ne ya yi, kuma za ki tsira da lafiyarki.

Idan kuwa wulaƙancin da zai yi ma ki ne matsalarki, ba ki da mafita sai haƙuri, domin shi zama na aure kowacce mace da irin tata jarrabawa, ta ki mai sauƙi ce, idan kin yi duba da ta wasu.

Allah Ya sani kin kauce wa yi wa abin hallita biyayya wurin saɓa wa mahallici, don haka Ina mai tabbatar mi ki ba za ki yi nadama ba.

Ku aiko da tambayoyinku ta [email protected] ko [email protected]