Sin ta bayyana kalaman jakadan Amurka a Sin a matsayin shaidar dake nuna tunani irin na danniya

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, ya ce kalaman da jakadan Amurka a Sin Nicholas Burns ya yi a lokacin wata zantawa da kafar watsa labarai ta CNN a kwanan nan, na nuni ga irin tunani na danniya da Amurka ke da shi.

Jami’in na Sin ya ce, yayin zantawar Burns da kafar ta CNN, ya tabo batun ziyarar kakakin majalissar wakilan Amurka a yankin Taiwan, inda ya sauya fari zuwa baki, yana mai cewa an zuzuta lamarin fiye da kima.

Ƙasar Sin ta gabatar da kakkausan ƙorafi ga Amurka a lokuta daban-daban, don gane da ziyarar Pelosi a Taiwan, tana mai bayyana cewa, Amurka ce za ta ɗauki alhakin abun da zai biyo bayan haramtacciyar ziyarar.

Fassarawar Saminu Alhassan