Ƙulla dangantaka da Ƙasar Sin domin samun sakamakon moriyar juna cikin sauri

Daga CMG HAUSA

Ranar 21 ga watan Augusta, muhimmiyar rana ce ga shawarar Ziri D’Ɗaya da Hanya Daya.

A wannan rana, jirgin kasan ƙasar Sin ya tashi daga tashar ƙasa da ƙasa ta Xi’an dake yammacin ƙasar, ya nufi birnin Hamburg na Jamus.

Wanda ya zama karo na 10,000 da jirgin ƙasa na ƙasar Sin ya je Turai a bana.

A kuma ranar ce, aka fara fitar da jiragen ƙasa masu sauri na ƙasar Sin a hukumance, inda aka tura jiragen ƙasa masu amfani da lantarki da jerin jiragen gwajin layin dogon Jakarta zuwa Bandung, daga tashar ruwa ta Qindao ta kasar Sin.

Fitar da jirgin ƙasa mai sauri na kasar Sin, ya buɗe wani muhimmin babi.

Fassarawar Fa’iza Mustapha