Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Gidauniyar TY Buratai Humanitarian Foundation da ke da shelkwata a Jihar Nasarawa, ta bayar da gudunmawar Naira 250,000 ga Mahajjaciyar jihar Zamfara, Hajiya Aisha Muhammad Yanguru Nuhuche, wadda ta tsinci Dala 80,000 kwatankwacin sama da Naira miliyan 84 sannan ta maida kuɗin ga mahukunta a ƙasa mai tsarki.
Gidauniyar ta kuma karrama ta da takardar shaidar karramawa a matsayin Jakadiyar Gaskiya.
A nasa jawabin shugaban gidauniyar, Hon. Ibrahim Dahiru Ɗanfulani a hedikwatar hukumar alhazai ta jihar Zamfara da ke Gusau, ya bayyana cewa, abin da Hajiya A’isha ta yi ta cancanci yabo.
Ya ce, an kafa gidauniyar ne domin yin koyi da irin ayyukan jinƙai da tsohon babban hafsan soji, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi a matsayinsa na uba ga gidauniyar wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya ga hidimta wa al’umma da al’ummarsa.
“An kafa wannan gidauniyar ce domin yin koyi da ayyukan jinƙai na tsohon shugaban hafsan Sojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai CFR, Garkuwan Keffi, Ƙauran Gusau wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya ga al’ummarsa,” in ji Ɗanfulani.
Ya ci gaba da cewa, gidauniyar ta yi fice wajen taimaka wa marasa galihu, marayu da zawarawa, sannan tana kula da gudunmawar al’umma don taimaka wa mutane su ƙara ƙarfi a fannoni daban-daban ta hanyar yaba ƙoƙarinsu.
Daga nan, Ɗanfulani ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zaburar da su wajen raya gaskiya da riƙon amana a cikin rayuwa ta yau da kullum da kuma yin zaɓin da zai yi tasiri ga rayuwar jama’a.
A cewarsa, hukumar alhazai ta jihar tana nuna gaskiya da gaskiya ta hanyar da za a yi shiru yayin da take mayar da maƙudan kuɗaɗen ga hukumar Saudiyya.
A jawabin godiya, kwamitin aikin Hajjin 2023 na jihar da Amirul Hajj Alh. Nusa Mallaha, ya gode wa gidauniyar bisa wannan karamci da karramawar da aka yi wa Hajiya Aisha Muhammad Yanguru Nuhuche.