Kano: Za a kammala titin Wuju-wuju, Kasuwar Kwankwaso nan ba da daɗewa ba – Kwamishina

Daga RABIU SANUSI a Kano

Kwamishinan Ma’aikatar Bibiyar Ayyuka da Nazari na Jihar Kano, Hon Ibrahim Namadi Dala, ya tabbatar da yunƙurin gwamnati Jihar Kano wajen ƙarasa ayyukan da ta sa gaba na Titin Wuju-Wuju da Kasuwar Zamani dake Garin Kwankwaso a Ƙaramar Hukumar Madobi da ma wasu ayyukan.

Ibrahim Namadi ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Laraba yayin da ya fita rangadin duba ayyukan da ba a kammala ba da aka fara tun lokacin Dr Rabiu Musa Kwankwaso da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta yi watsi da su.

Namadi ya ce, babu abun bacin rai da ya samu sai lokacin da ya ziyarci makarantar koyon kere-kere da ke Ƙaramar Hukumar Madobi da ya samu gaba ɗaya makarantar ta lalace sai dai aka samu fara gudanar da je-ka-ka-dawo a cikinta.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, a cikin makarantar akwai ɗalibai 700 amma malaman dake koyarwa ta din-din-din guda huɗu ne kacal, sannan an kuma bi makarantar an ƙwace wasu daga cikin kayan aikinta, tare da lalacewar wani sashe na gininta.

“Yadda muka zagaya Kama daga titin Wuju-wuju, ofishinmu na din-din-din, makarantar koyan aikin lafiya da kasuwar zamani ta Kwankwaso da sauran guraren da muka kewaya za mu miƙa rahoto akan abinda muka gani dan ɗaukar mataki.”

Namadi Dala, ya buƙaci ‘yan kwangilar da aka ba ƙarasa ayyukan nan da su tsaya tsakaninsu da Allah wajen gudanar da aikin mai nagarta kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarce su da yi.