Gobe Talata Matawalle zai yi bikin komawa APC

Daga WAKILINMU

Gobe Talata idan Allah ya kai mu Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Babban daraktan gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Gusau a Lahadin da ta gabata.

A cewar Idiris, “An kammala shiri na sauya sheƙar gwamnanmu daga PDP zuwa APC.

“Baki ɗayan kwamitocin da aka kakkafa domin bikin duk sun ba da bayanin komai na tafiya daidai don tabbatar da bikin ya gudana ciki nasara a Gusau a ranar Talata, 29, Yuni.”


Ya ƙara da cewa komawar Matawalle APC zai ƙara wa jam’iyyar tagomashi a jihar.

Idris ya ce kasancewar gwamnan mai jama’a, zai koma APCn ne tare da masoyan nasa a matakai daban-daban, kama daga wasu ‘yan majalisar dokokin jihar su 18 zuwa shugabannin PDP na jihar da sauransu.

Daga nan, ya ce shugaban riƙo na jam’iyyar APC, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni tare da muƙarrabansa su  ne ake sa ran su karɓi Matawalle zuwa APC yayin bikin.