IPMAN ta musanta shirin tafiya yajin aiki

*Alhaji Fari ya buƙaci ‘yan ƙasa su kwantar da hankalinsu

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (IPMAN) ta ce ba ta da wani shirin shiga yajin aiki ko aniyar rufe gidajen mai a faɗin ƙasa. Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Alhaji Sanusi Fari, shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Awka wadda ta sami sa hannun sakatarenta na ƙasa, Mr Chidi Nnubia, Fari ya buƙaci al’ummar ƙasa da su yi watsi da duk wani bayani da ke nuni da IPMAN na shirin tafiya yajin aiki.

Ran Litinin a Abuja aka jiyo Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙungiyar na Ƙasa, Alhaji Yakubu Suleiman, ya yi barazanar cewa IPMAN za ta tafi yajin aiki tare da rufe gidajen mai a faɗin ƙasa daga ranar Talata wai saboda kwanton ɓaunan da ‘yan sanda suka yi wa sakatariyarsu.

Suleiman ya yi zargin cewa ‘yan sanda sun yi wa babban ofishin IPMAN kwanton ɓauna a Juma’ar da ta gabata ba tare da wani dalili ba.

Ya ce ‘yan ƙungiyar wanda ransu a ɓace yake game da haka, sun yi taro kan batun a matakai daban-daban tare da barazanar cewa za su rufe kafatanin gidajen mai a faɗin ƙasa muddin ba a magance matsalar ba.

Sai dai shugaban IPMAN na ƙasa, Alhaji Fari, ya yi kira ga ‘yan kasuwar fetur da ma al’ummar ƙasa baki ɗaya da su yi watsi da kalaman Suleiman.