Sun harbe mai juna-biyu sun yi garkuwa da mijinta a Kwara

Daga AISHA ASAS

Rahotanni daga jihar Kwara sun tabbatar cewa a ranar Asabar da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun harbe wata mai juna-biyu har lahira kana suka yi garkuwa da magidanta.

Lamarin wanda ya auku a yankin ƙaramar hukumar Offa na jihar, an ce ‘yan bindigar sun harbe Hawa ɗauke da juna-biyu sanan suka yi awon gaba da maigidanta, Lukman Ibrahim.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna mummunan al’amarin ya auku ne a daidai lokacin da Lukman da surikinsa da matar tasa da kuma wani ɗansa suke mota za su koma gida ran Asabar da daddare.

Sahaidu sun tabbatar cewa ‘yan bindigar sun farmaki Lukman da ahalinsa ne a hanyar Ojoku wanda tsakanin wurin da ofishin ‘yan sanda babu nisa.

An ce nan take matar ta ce ga garinku nan sakamakon harbi da bindiga da ‘yan bindigar suka yi mata inda daga bisani aka ɗauki gawarta zuwa babbar asibitin Offa.

Sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa ‘yan bindigar suka halaka matar nan take sannan suka ƙyale surikin da ɗan ba.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare da cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta sunkuya bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *