Shinkafi, ciyamomin APGA 14 da na mazaɓu 147 sun bar APGA zuwa APC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Babban Sakataren Kwamitin amintattun na ƙasa na Jam’iyyar APGA, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi tare da shugabannin ƙananan hukumomi 14, na Jami’iyyar, shugabannin mazaɓu 147 a jihar Zamfara sun fice daga jam’iyyarsu ta APGA kuma sun bi gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle zuwa Jami’iyyar APC mai mulki a ƙasar nan.

Shinkafi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a gidansa da ke Gusau yayin da yake jawabi ga shugabannin zartarwar jihar na APGA wanda ya haɗa da dukkanin shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi 14, shuwagabannin mazaɓu 147 waɗanda su duka suka sauya sheƙa daga jam’iyyarsu suka bi gwamnan Zamfara Matawalle zuwa APC.

A cewarsa, tun daga shakarar 2002 aka yi wa APGA rijista kimanin shekaru 19 da suka gabata a matsayin babbar jam’iyya mai rijista a ƙasar, ya ƙara da cewa tun daga wannan lokacin, bai taɓa canza jam’iyyarsa zuwa wata ba duk da yanayin siyasa.

Ya ci gaba da cewa, ya bar APGA ne don ya taimaka wa Gwamna Bello Mohammed Matawalle don bunƙasa jihar a dukkan ɓangarorin tattalin arziki domin ci gaban mutanen kirki na Jihar Zamfara.

“Ba mu shigo APC ba ne don tara abin duniya kuma za mu bayar da gudummawa matuƙa wajen ganin kowane ɗan jihar Zamfara ya ci gajiyar romon dimokiraɗiyya tare da magance matsalolin rashin tsaro da muke fuskanta a jiharmu ta mu mai albarka”. Inji Shinkafi

Manhaja ta ruwaito cewa, Shinkafi tsohon ɗan takarar Gwamna na APGA kuma Sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar ta APGA na ƙasa watau (BOT) a cikin wata wasiƙa zuwa ga Sakataren Jam’iyyar na ƙasa a makon da ya gabata, ya sanar da murabus ɗinsa a matsayin mamba na jam’iyyar kuma Sakataren Jam’iyyar .

Ya ƙara da cewa, “Na yanke shawarar yin murabus ɗin ne bayan tuntuɓa da na yi da magoyan baya na, da dangi na, da abokaina na siyasa a jihar ta Zamfara da sauran ‘yan Nijeriya waɗanda suka kafa ɓangare na na goyon baya”.

A nasa jawabin, Hon. Bello Maijama’a ya ce, gaba ɗaya sun amince su sauka a matsayinsu na shugabannin APGA a jiharta Zamfara waɗanda suka haɗa da dukkanin shugabannin ƙananan hukumomi 14 da shugabannin mazaɓu 147 na APGA tare da dukkan magoya bayan jam’iyyar a jihar sannan suka bi Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi da Gwamna Bello Mohammed Matawalle zuwa APC don ci gaban jihar Zamfara ta fuskar zamantakewa, tattalin arziki da siyasa.

A jawabinta, shugabar matan jihar ta APGA, Hajiya Halima Abdullahi ta ce, dukkan mata daga APGA a jihar sun haɗa kai suna mara wa Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi da Gwamna Bello Mohammed Matawalle baya ga jam’iyyar APC saboda jin daɗin mata masu rauni a jihar da ci gaban jihar jihar gaba ɗaya.

Idan za a iya tunawa, Gwamnan Zamfara ya bayyana ƙudurinsa na ficewa daga jam’iyyar sa ta PDP zuwa jam’iyyar APC a gobe Talata Wanda bikin zai gunana a Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara, yayin da ake sa ran gwamnonin APC 18 ne za su halarci bikin karɓarshi.