Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya buƙaci Rundunar Sojin Nijeriya ta kafa ƙarin sansanonin sojoji na musamman a wasu yankunan jihar da ke fama da matsalar rashin tsaro, domin dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka da suka addabi al’umma.
Musamman, gwamnan ya buƙaci kafa bataliya ta musamman a yankin Alkaleri, yana mai cewa ’yan bindiga na fitowa daga dazuzzukan yankin dauke da makamai tare da amfani da motoci masu yawa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya ce muhimmancin yankin ya ƙara kasancewa ne saboda dazuzzukan Alkaleri suna da kusanci da wasu jihohi biyar na arewacin Nijeriya, lamarin da ke buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaro.
Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Tsaro ta Jihar Bauchi da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi, da kuma lokacin da Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Nijeriya ta 3 Diɓision da ke Jos, Manjo Janar Maɗwell Dangana, ya kai masa ziyarar ban girma.
Gwamna Bala ya ce ana buƙatar kafa sansanonin sojoji a yankunan Tafawa Balewa, Bogoro, Alƙaleri da Katagum, saboda muhimmancin waɗannan wurare wajen tabbatar da tsaron jihar.
Ya ce kafa waɗannan sansanonin sojoji tare da ƙarfafa Rundunar ’Yan Sanda da sauran jami’an tsaro zai taimaka wajen tinkarar matsalolin tsaro, musamman a wuraren da har yanzu ba su da isassun ofisoshin ’yan sanda.
Gwamna Bala ya ce ya tattauna batun da Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Nijeriya ta 3 Diɓision, Manjo Janar Maɗwell Dangana, a lokacin da ya kai masa ziyarar ban girma, yana mai cewa Dangana tsohon ɗalibinsa ne a Kwalejin FGC Azare, inda ya taɓa koyarwa.
Ya jaddada cewa gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro tallafin kayan aiki da ababen more rayuwa, tare da yin haɗin gwiwa da al’umma, masarautu da masu kishin jihar Bauchi wajen gina ofisoshin ’yan sanda a wuraren da ake buƙata.
Ya ce, “Ba wai muna ba da goyon baya da baki kawai ba; muna mayar da goyon bayanmu zuwa ayyuka na zahiri ne don samun ingantaccen tsaro.”
Gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen gudanar da ayyukan haɗin gwiwa, musamman sintiri, tattara bayanan sirri da sa ido kan dazuzzuka, kasuwannin karkara da yankunan kan iyaka.
Ya ce hakan zai taimaka wajen daƙile yunƙurin masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga na kafa sabbin sansanoni a jihar, domin faɗaɗa ayyukan ta’addanci da ci gaba da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
