Gwamna Bello ya yi rigakafin korona kashi na biyu

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yi allurar rigakafin korona na Oxford Astrazeneca karo na biyu. Bello ya yi rigakafin ne yayin ƙaddamar da shirin rigakafin karona karo na biyu a jiharsa.

A lokacin ƙaddamar da shirin wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, an ga mataimakin gwamnan da sauran mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar su ma sun yi tasu allurar karo na biyu-biyu.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan da ya yi allurar, Gwamna Sani Bello ya nuna gamsuwarsa kan yadda jama’ar jiharsa suka bada haɗin kai yayin rigakafin zubin farko. Tare da ƙarfafa wa waɗanda suka samu yin na farkon gwiwar yin na biyun saboda a cewarsa, rigakafin ba ya ɗauke da wata illa.

“Ina mai tabbatar wa kowa cewa allurar ba ta da wata illa. Kowa ya je ya yi, hakan zai kare lafiyarku da ta masoyanku. Musamman dattawa, ya kamata su je su yi,” in ji Bello.

Tun farko a jawabinsa, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr. Muhammad Makusidi, ya ce kawo yanzu jihar Neja ta karɓi allurar rigakafin cutar korona guda 89,600.

Ya ci gaba da cewa, allura 44,860 ne aka yi wa jama’a a kashin farko, sannan akwai wadataccen maganin da za a yi wa mutane allurar a karo na biyu. Ya ce ana kyautata zaton duka waɗanda suka cancanci samun allura ta biyu za a yi musu baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *