Gwamna Ganduje: Shin dankali sha kushe ne..?

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya (Dr.) Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake yi wa laƙabi da Khadimul Islam, ya kasance gwamnan da ya ke jagorantar jiha mafi yawan jama’a a Nijeriya kawo yanzu kusan tsawon shekara bakwai kuma a yanayin tafiyar siyasar da ake yi zai shekara takwas yana jan ragamar mulkin jihar, idan da rai, lafiya da nisan kwana.

Tabbas ko da ba a faɗa ba, jiha kamar Kano za ta iya yin wahalar tafiyarwa, saboda yanayin yawan al’ummar da ta ke da shi da kuma zafin siyasa ta aƙida da aka san Kanawa da ita.

Kusan za a iya cewa, babu wani gwamnan farar hula da ya mulki jihar da ba a taɓa jifan sa ba a lokacin da ya ke kan mulki, banda tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, to amma shi ma sai da ya kasa sanya jam’iyyarsa ta lashe zaɓe a lokacin da ya so Malam Salihu Sagir Takai ya gaje shi a kujerar mulkin jihar.

Hatta Marigayi Alhaji Muhamamdu Abubakar Rimi da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso sun sha wahalar Kanawa lokuta daban-daban da suke mulkin jihar. Dukkansu ba su iya lashe zaɓe a zango na biyu da suka nema ba. Ba a maganar tsohon gwammnan jihar, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, wanda har yanzu wasu na ganin cewa, Kanawan su na haƙon sa, duk da cewa, ya jima yana wakiltar Yankin Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya.

Yanzu dai Ganduje ya shafe kusan shekara bakawai yana mulkar Kano, ba a tava jifan sa ba, amma za a iya cewa, ba a fasa sukar sa ba, kuma zaɓe bai zo ba ballantana a gane ƙarfin ƙwanjinsa wajen dasa wanda ya ke so ya gaje shi. Wato dai hakan ya na nuna cewa, har yanzu gwamnan bai kai gargarar da tsofaffin gwamnoni jihar suka taɓa kaiwa ba. Babba abin tambaya shine, shin Gwamna Ganduje zai kai waccan gargara ko kuwa a’a?

A fili dai ta ke cewa, gwamnan na Kano ya na gudanar da manyan ayyukan cigaba a jihar. A gaskiya babu tantama kan hakan, domin duk da irin matsalolin ƙarancin kuɗi da jihohin Nijeriya ke fuskanta, saboda rashin samun isassun kuɗi daga Asusun Tarayya da ake raba musu duk wata, zai yi wahala ka je wata jiha ka ga a na aiwatar da manyan ayyukan masu yawa irin yadda ake yi a Kano lokacin Ganduje.

To, sai dai kuma idan ka tattauna da ’yan adawa da ma wasu waɗanda ba ’yan adawarsa ba ne, su na matuƙar sukar gwamnan, su na wassafa shi a matsayin gwamna mafi muni da aka tava yi a jihar. A lokaci guda kuma, mabiyansa da ma wasu waɗanda ba mabiyan nasa ba ne, su na kwatanta shi da Gandun Aiki! Shin mene ne ya janyo hakan?

Za mu cigaba a makon gobe idan hali ya yi!