Rahotanni daga ƙasar Ingila na nuni da cewa Sarauniya Elizabeth ta kamu da cutar korona. Fadar Buckingham ce ta bada sanarwar faruwar hakan.
Bayanan fadar sun nuna sarauniyar na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa.
Fadar ta bayyana a cikin sanarwar tata cewa, “Za a ci gaba da duba sarauniyar kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace.”
BBC ta ruwaito cewa Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta haɗu da babban ɗanta kuma magajinta, wato Yarima Charles wanda shi ma ya kamu da korona a makon da ya gabata.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan da sarauniyar ta kafa tarihi ta zama wadda ta fi daɗewa kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ingila bayan da ta cika shekara 70 a kan mulki a ranar 6 ga watan Fabrairu.
A bayyane yake cewa sarauniyar ta yi riga-kafin korona zagaye na farko da na biyu.