Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa ya sake hira da ‘yan jaridun CMG

Daga CRI HAUSA

Kafin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na bana a Beijing, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa wato IOC, Thomas Bach ya sake zantawa da ‘yan jaridun CMG, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin.


Bach ya bayyana cewa, ‘yan wasannin ƙasa da ƙasa sun shaida wa duniya kyawawan halayensu, da bayyana ma’anar zumunci da samun fahimtar juna da zaman lafiya. Alal misali, ‘yan wasannin Ukraine da Rasha sun rungumi juna, kana, ‘yan wasan ƙasar Sin sun goyi bayan ‘yan wasan Amurka, har sun ba su tambarin Olympics kyauta don nuna son karɓar baƙi. Akwai irin waɗannan misali da dama, waɗanda suka nuna cewa wasan Olympics za su iya yin galaba kan fito-na-fito na rikicin siyasar duniya.

Mista Bach ya ƙara da cewa, kafar CMG ta samu gagarumar nasara wajen gabatar da shirye-shirye gami da watsa rahotanni game da gasar ta bana, kuma yana da yakinin cewa haɗin-gwiwar IOC da CMG za ta daɗa inganta.

Fassarawa: Murtala Zhang