Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tsayar da Mataimakinsa, Nasir Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyar APC a zaɓen 2023.
Ganduje ya zaɓi Gawuna ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a gidan Gwamnatin Kano,
Kazalika, masu ruwa da tsakin sun kuma amince da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo, ya zama mataimaki a takarar ta Gawuna.
Majiyar mu ta jiyo cewa da ƙyar masu ruwa da tsaki da wasu manya a jihar su ka shawo kan Garo ya amince da yi wa Gawuna mataimaki a takarar.
Murtala Garo dai ana ganin ya na da tasiri a jam’iyyar a matakin Ƙananan Hukumomi, shi ne ɗan takarar da mai-ɗakin gwamnan, Hafsa Ganduje ta zaɓa a matsayin ɗan takarar APC a jihar.
