Gwamnatin Tarayya da ASUU za su ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar malaman Jami’o’i (ASUU) da suke yajin za su ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa. Tattaunawar za ta kasance da nufin kawo ƙarshen dogon yajin aikin da ƙungiyar take yi wanda ya jawo rufe dukkan jami’o’in mallakin gwamnatin Nijeriya na tsahon lokaci.

Ministan ƙwadago da aiki na Nijeriya, Dakta Chris Ngige shi ya bayyana haka a Abuja, a yayin da yake yin jawabin buɗewa a wani taro da gwamnatin ta shirya don jin ta bakin ɓangarorin guda buyu wato gwamnati da kuma ƙungiyar Malaman jami’o’i da suke yajin aiki.

Dakta Ngige ya bayyana cewa, su kansu ƙungiyoyin ilimi a ƙasar nan ba su da haɗin kai a tsakaninsu. Domin a cewar sa, da a ce ƙungiyoyin da suka shafi harkar ilimi za su buɗe ƙofar fahimtar juna a tsakaninsu, da an kauce wa rashin fahimta da dama a harkar ilimi da kuma tsakanin ƙungiyoyin da suka shafi ilimi. Inda ya buga misali da ɓangaren ilimi a halin yanzu. A cewar sa an samu zaman lafiya da salama tsakanin ƙungiyoyin su saboda haɗin kai da fahimta.

Hakazalika, ministan ya ƙara da cewa, adawar da take tsakanin ɓangarorin ilimin ba za ta haifar da komai ba. Domin kowanne ɓangare a fannin ilimi yana da amfani, kuma ba zai yiwu a yi tafiyar babu shi ba. Sannan a cewar sa gwamnati tana nan tana ƙoƙarin yadda za ta tunkari matsalolin ta yadda za a ba kowanne ɓangare haƙƙinsa.

Dakta Ngige ya qara da cewa, da ma matsalolin ba wasu matsaloli ne ba, illa matsalolin da suke da alaƙa da kuɗi da kuma harkar walwala.

Shi ma shugaban ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da aka zauna da su, NAAT, mai suna kwamared Ibeji Nwokoma ya bayyana cewa, su ma ba wai don suna sha’awar yajin aikin suka tafi ba, sun tafi ne saboda ba yadda suka iya. Domin Ma’aikatar ilimi sam ta ai taɓuka komai a kan matsalolinsu.

Kuma a cewar sa sun tafi yajin aikin ne don su jawo hankalin gwamnati ta fuskanci matsalolin da suke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *