Daga AMINA YUSUF ALI
Daraktan kamfe ɗin Bola Ahmad Tinubu, Honarabul Jubril Abdulmuminu Kofa ya bayyana shirinsa na barin jam’iyyar mulki ta APC.
Kofa wanda yana cikin na gaba-gaba a wajen kamfe ɗin Tinubu, ya ce ya yi dukkan iya ƙoƙarin da zai yi ga jam’iyyar APC.
Tun a farkon shekarar nan ne dai aka ba da sanarwar naɗin Kofa a matsayin darakta janar na kamfe ɗin Tinubu. Amma sai ga shi an wayi gari saƙonsa na canza sheƙar siyasa.
Kofa, ya yi amfani da shafinsa na Tiwita don sanar da al’umma wannan hukuncin da ya yanke na barin APC. Amma ɗan siyasar wanda ɗan asalin Kano ne har yanzu bai ba da sanarwar sabuwar jam’iyyar da ya koma ba. Sai dai a wani rubutu da ya sake wallafawa, ya ce zai bayyana sabuwar jam’iyyarsa nan da awannin 24.
Kofa ya bayyana cewa: “Na yi iya ƙoƙarina ga APC. Lokaci ya yi da zan ƙara gaba. Zan kuma sanar da sabuwar jam’iyyar da na koma, nan da sa’o’i 24, insha’Allah. Zan ba da sanarwar nan ba da daɗewa ba”.
Abdulmumin Jibrin Kofa tsohon ɗan majalisa ne na majalisar dokoki ta tarayyar Nijeriya mai wakiltar Ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji a tsakanin shekarar 2015 da 2019.
Ɗan majalisar ya sha fafatawa da shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano, abinda ake ganin ya sa ya cire kansa daga shiga sabgar zaɓen shekarar 2019.
Daga baya ne kuma aka naɗa shi a matsayin daraktan zartarwa na hukumar tsara gine-gine (FHA).
Duk da dai har yanzu ɗan siyasar bai buɗe baki ya faɗi ainahin dalilin da ya sa ya sauya sheƙa ba, amma wasu rahotanni sun bayyana cewa, sauya shekar tasa ba ta rasa nasaba da yadda wasu manyan shugabannin APC a Kano suka ƙi mara masa baya wajen tsayar da shi a matsayin ɗan takarar Gwamnan jihar a zaɓen mai zuwa na 2023.
Haka rahotannin sun yi hasashen cewa, ana tsammanin zai koma zuwa jam’iyyar PDP ne.
