Ya fi kyau ‘yan siyasar Birtaniya su maida hankali kan harkokinsu

Daga CMG HAUSA

Ranar 7 ga wata, an ƙaddamar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi a Northern Ireland na ƙasar Birtaniya, inda jam’iyyar Sinn Féin da ke neman raba Northern Ireland daga Birtaniya ta fi samun kujeru, ta zama jam’iyya mai kare muradun al’umma da ta fi samun kujeru a majalisar dokokin Northern Ireland cikin shekaru 101 da suka wuce. Manazarta sun yi bayani cewa, nasarar da jam’iyyar Sinn Féin ta samu ta bai wa gwamnatin Birtaniya wata matsala ta daban.

Bayan ɓarkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, gwamnatin Birtaniya ta yi kasala wajen yaƙi da annobar. A watan Febrairun bana, ta sanar da mayar da annobar a matsayin wani nau’in cuta mai kamawa, a maimakon mummunar cuta mai kamawa, lamarin da ya sa jimillar yawan mutanen da suka mutu sakamakon annobar ya kai kusan dubu 180 a Birtaniya.

Ban da haka kuma, Birtaniya na fuskantar matsaloli da dama wajen raya tattalin arziki sakamakon annobar, da matsala a tsarin samar da kaya, da ƙarancin ‘yan ƙwadago, sakamakon janye kanta daga ƙungiyar EU da kuma hauhawar farashin makamashi. A ranar 5 ga wata, bankin Ingila ya yi kashedin cewa, a bana yawan hauhawar farashin kaya zai iya wuce kashi 10% a Birtaniya. An ƙiyasta cerwa, adadin zai kafa tarihi cikin shekaru 40 da suka gabata. Kila tattalin arzikin ƙasar zai samu koma baya a shekara mai zuwa.

Amma yayin da waɗanda ke mulkin ƙasar suke fuskantar wahalhalu a gida da wajen Birtaniya, sun yi yunƙurin nuna karfi ga ƙasashen duniya a maimakon yin tunani kan matakan da za a ɗauka. Ya fi kyau ‘yan siyasar Birtaniya su mai da hankali kan harkokinsu.

Fassraawa: Tasallah Yuan