Hong Kong za ta samu kyakkyawar makoma bisa sabuwar surarta da sabon tsarin zaɓe

Daga CMG HAUSA

Ofishin kula da al’amurran yankunan musamman na Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar ƙasar Sin ya sanar a yau Lahadi cewa, Hong Kong ta koma sabuwa yayin da aka aiwatar da sabon tsarin zaɓe, lamarin da ke ba da tabbacin samun sabuwar makoma, gami da bude sabon shafi na ci gaban yankin.

Ofishin ya bayyana hakan ne a wani sharhi da aka wallafa bayan lashe zaɓen da Lee Ka Chiu John ya samu a matsayin kantoman yankin Hong Kong na shida, bayan da ya samu ƙuri’u da babban rinjaye. Ofishin ya kuma miƙa saƙon taya murna ga Lee Ka Chiu John bisa samun nasara a zaben.

A cewar ofishin, zaɓen na sabon kantoman yankin, wata babbar nasara ce ga sabon tsarin zaɓen yankin musamman na Hong Kong tun bayan zaɓen kwamitin shirya zaben a watan Satumban bara, da kuma zaɓen kwamitin kula da ayyukan kafa doka na yankin karo na 7 wanda aka gudanar a watan Disamban bara.

Ofishin ya ƙara da cewa, haƙiƙanin abubuwa sun shaida cewa, sabon tsarin zaɓen tsari ne mai kyau, wanda yake bin manufar “ƙasa ɗaya amma tsarin mulki biyu” kuma ya dace da haƙiƙanin yanayin Hong Kong.

Ofishin ya ci gaba da cewa, gaskiya za ta yi halinta cewa sabon zaɓaɓɓen kantoman yankin Hong Kong zai ba da jagoranci ga sabuwar gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da jama’ar dukkan bangarorin al’ummun yankin, da su hada kansu sosai domin samar da kyakkyawar makomar tafiyar da harkoki yadda ya kamata a Hong Kong a bisa sabon mafari.

Fassarawa: Ahmad