Gwamna Raɗɗa ya bayyana shirye-shiryen ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa matasa a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, bisa irin jagorancin hangen nesa da yake bayarwa wajen inganta ƙirƙire ƙirƙire, sana’o’i da kuma bai wa matasa damar ci gaba.

Shettima ya bayyana Jihar Katsina a matsayin “fitila ta ƙirƙira da juriya a Arewacin Nijeriya,” yana mai cewa jihar na farfaɗo da tsohon gadon ta na ilimi, kasuwanci da fasaha.

Yayin da yake jawabi a bikin kammala karatun Dikko Social Innovation Academy (DSIA) da kuma ƙaddamar da kyaututtukan Katsina MSME karo na farko a ɗakin taro na gidan gwamnati, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yabawa Katsina saboda kyakkyawan tarihinta a fagen ilimi da al’adu, wanda ya taimaka wajen gina Arewacin Nijeriya tsawon ƙarni.

Ya tuna da yadda Katsina ta kasance cibiyar malamai, sarakuna da ‘yan kasuwa, a cewar sa Sheikh Mohammed Bello ya rubuta Usul Siyasa domin Sarkin Katsina — littafin jagora a harkar mulki tun kafin mulkin mallaka.

Sanata Shettima ya kuma ce Kwalejin Katsina wadda daga baya aka sani da Barewa College, ta haifi fitattun shugabanni a Nijeriya, alamar yadda jihar ke da zurfin tarihi na ilimi da shugabanci.

A cewar Shettima, wannan ruhin ƙirƙira da ƙwazo har yanzu yana cikin mutanen Katsina,”ga su manoma ne masu sana’a da matasa masu kasuwanci, waɗanda ke nuna jajircewa wajen fuskantar ƙalubale.

Ya buƙaci a ƙara mayar da hankali wajen ƙera masana’antu daga albarkatun cikin gida kamar auduga da gero, domin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa ƙoƙarinsa na ƙarfafa harkokin ƙanana da matsakaitan masana’antu (MSME) ta hanyar hukumar ci gaban Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA), yana mai cewa wannan shiri ya yi daidai da tsarin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya kuma yaba wa Gwamnan bisa ƙoƙarinsa na haɗa kan shugabannin siyasa da na gargajiya a faɗin jihar, yana mai cewa:
“Ba mu da wani dalili na yin gaba da juna — dole mu haɗa kai don yaƙi da talauci da rashin tsaro.”

Cikin dariya, Shettima ya ƙara da cewa:
“Ina alfahari da haɗin kan Katsina da ci gaban ta — kuma dole in faɗi gaskiya, “gwamnan ya fi kama da ni fiye da kowa cikin wannan ɗaki!,”Shettima ya ce.

Shettima ya gode wa al’ummar Katsina bisa tarba da karamci, yana kiran jihar da “gida mai ƙasar tarihi, haɗin kai da fata mai kyau.”

A nasa jawabin, Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce manufar gwamnatin sa ta mayar da hankali ga ƙirƙira da kasuwanci tana canza rayuwar matasa a jihar. Ya bayyana taron da cewa:
“Biki ne na ƙirƙira, juriya, da ci gaba zuwa makoma mai albarka.”

Ya ce tun lokacin da suka hau mulki, sun ɗauki mataki na musamman na bai wa mutane ƙarfi ta hanyar sana’a da kirkira, wanda hakan ya haifar da KASEDA — wadda a yau ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ci gaban kasuwanci a Nijeriya.

Malam Dikko Raɗɗa ya yaba wa Hajiya Aisha Aminu, Darakta Janar na KASEDA, bisa jagorancin ta, yana cewa tana daga cikin mata masu hazaƙa a hidimar gwamnati a Nijeriya. Ya ce ta jagoranci fitar da tsarin ci gaba na shekaru biyar, wanda ya yi daidai da tsarin tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana Dikko Social Innovation Academy (DSIA) a matsayin ɗaya daga cikin muhimman shirye-shiryen gwamnati, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa daga yankunan da ba su da dama horo na aikace-aikace don magance matsalolin al’umma.

Gwamnan ya ce an samo ra’ayin daga Uganda, inda wasu matasa uku ‘yan Katsina suka tafi domin nazarin tsarin Social Innovation Academy (SINA) da ake yabawa a duniya.

“Yau ina alfahari da ganin fitowar ɗaliban farko 18, waɗanda suka kammala watanni shida na horo a fannin ƙirƙira sana’a, tunani na tsara mafita, da warware matsaloli.

Gwamnan ya ƙaddamar da ɗalibai na farko 18 da suka sami horo na tsawon watanni shida ƙarƙashin shirin DSIA.

Daga baya mataimakin shugaban ƙasa ya buɗe taron masu ruwa da tsaki kan ƙanana da matsakaitan sana’o’i da buɗe hanyar da taso daga masallacin juma’a na kofar soro zuwa WTC mai tsawon kilomita 3.

By ukarofi