Gwamna Uba Sani ya yi sabbin naɗe-naɗe a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya sake naɗa Sakataren gwamnatin jihar a ƙarƙashin gwamnatin Nasir El-Rufai Balarabe Lawal a muƙaman gwamnatinsa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Gaɗa Labaran Gwamnan, Mohammed Shehu, ya fitar a ranar Talata, inda ya ce, Lawal ya ci gaba da riƙe muƙamin a bisa la’akari da gogewarsa aikinsa a harkokin mulki domin ya taimaka wajen tafiyar da sabuwar gwamnati cikin sauƙi.

Uba Sani ya kuma amince da naɗin Shuaibu Gimi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Sadarwa da kuma Nasir Abdulkadir a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai, yayin da Dahiru Ahmed zai kasance babban mataimaki na musamman kan kafafen sadarwa na zamani.

Haka zalika, gwamnan ya amince da naɗin tsohon Kwanturolan Shige da Fice na Jihar Kano, Sani Liman, a matsayin sabon shugaban ma’aikatansa, yayin da aka naɗa Habiba Anana Shekarau a matsayin sabuwar shugabar ma’aikata.

Shekarau, wanda shine Babban Sakatare a Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi a yanzu, yana da gogewar sama da shekaru 30 a Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kaduna.

Sauran sun haɗa da Hafsah Aminu Ashiru – Sakatariyar Mataimakiyar Gwamna Naja’atu Garba Ahmed — Babban Mataimaki na Musamman (Ofishin Gwamna), Dakta John Danfulani — Babban Mataimaki na Musamman (Research & Documentation), da Samuel Mock Kure — Babban Mataimakin Gwamna Harkokin Jama’a).

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnan ya kuma riƙe ayyuka na sauran manyan jami’an gwamnatin Nasir El-Rufai domin samar da alaaa tsakanin gwamnatocin biyu.

Sun haɗa da Muhammad Hafiz Bayero wanda zai zama babban mashawarcin gwamna, yayin da Barista James Atung Kanyip da Chris Umar aka naɗa mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati. Dakta Shehu Usman Muhammad da Bulus Banquo Audu an naɗa su a matsayin mashawartan Gwamna.

Sanarwar ta ce, an yi naɗin ne saboda ganin cewa jihar na buqatar awararrun hannaye da mutane masu ilimi da za su taimaka wa sabuwar gwamnatin wajen cimma manufofinta na ɗorewa.

An bayyana cewa, sabbin waɗanda aka naɗa sun zo aikin ne tare da gogewa daban-daban, ƙwarewa da kuma sun tabbatar da bayanan gaskiya da kuma sadaukarwa ga aikin.

Don haka gwamnan ya buƙaci waɗanda aka naɗa da su ga naɗin nasu tamkar wani aiki ne, inda ya ƙara da cewa, mutanen jihar nagari suna tsammanin sakamako daga gare su, don haka dole ne su taka rawar gani.