Ma’aikatan sufurin jiragen ruwa sun shiga yajin aikin sai-Baba-ta-gani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Za a rufe tashoshin jiragen ruwa a Nijeriya yayin da Ƙungiyar Ma’aikatan Ruwa ta Nijeriya (MWUN) ta ayyana yajin aikin da ba a taɓa gani irinta ba a faɗin ƙasar.

Shugaban MWUN, Prince Adewale Adeyanju, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, 2023, ya buƙaci ɗaukacin mambobinsa da su rufe dukkan ayyukan kamfanonin sufurin jiragen ruwa tare da fara yajin aiki na dindindin a faɗin ƙasar daga ranar Litinin saboda taƙaddamar da ta kunno kai tsakaninta da kamfanonin sufurin jiragen ruwa dangane da ƙarancin albashi da jin daɗin ma’aikata.

Ya koka da cewa, tun shekarar 2018 ƙungiyar qwadago ta yi ta fama da kamfanonin jigilar kayayyaki a kan mafi qarancin albashi na kamfanonin jigilar kayayyaki kan jin daɗin ma’aikata ba tare da wata fa’ida ba.

A cewarsa, duk da wa’adin da tsohon Ministan Sufuri na aasar nan, Muazu Sambo ya yi, kamfanonin sufurin jiragen ruwa, waɗanda galibinsu na ƙasa da ƙasa ne, sun ƙi amincewa da hakan, yana mai nuna baƙin cikinsa da yadda yanayin aiki da ma’aikata ke yi a masana’antar sufurin jiragen ruwa ta ƙasa ke bautar da su.