Kasuwancinmu na yankin Afirka ya fi ko’ina riba – Bankin UBA Africa

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Bankunan UBA na Afirka ya bayyana yadda rukunin bankunan nasu suke cin mafi yawan riba a yankin Afirka fiye da ko’ina. Ya bayyana cewa, yankin Afirka yana ba wa bankin nasu ribar da ta kai kusan kaso 50 na dukkan cinikin da kamfanin nasu yake samu.

Daraktan zartarwa/Babban jami’in zartarwa na UBA a Afirka, Abiola Bawuah shi ya bayyana hakan.

Misis Bawuah ta qara da cewa, kowanne rseshe na bankin UBA a Afirka a zaune yake da ƙafafunsa. Wannan lissafi ma ya ahafi har da ƙasaahen Afirka wanda yaƙi ya illata su. Ko’ina dai ana samun nasara da cigaba a cewar sa.

Hakazalika a cewar ta kuma, Bankin UBA ya taka rawa sosai wajen ɗaukar nauyin samar da ababen more rayuwa, da kuma zuba sama da Dalar Amurka biliyan guda a faɗin Afirka. Musamman a ɓangaren asibitoci, lafiya, lantarki, tituna da sauransu. Kuma a cewar ta ma a hakan ma ba a lissafa da cigaban kasuwancin da bankin ya kawo a ƙasashen Afirka.

Haka, a cewar ta, kamfanin ya kasance mafi sanar da gurbin aiki a vangaren hada-hadar kuɗi ga ‘yan Afirka. Alƙalumma sun nuna, bankin ya samar da guraben ayyukan yi dubu 25 ga ‘yan Afirka. Kuma yana aiki tare da kwastomomi fiye da miliyan 35 a faɗin duniya.

Mista Bawuah ya yi wannan jawabi ne yayin tattaunawa da manema labarai da ‘yan jaridu daga ƙasashens Afirka daban-daban a wani taron manema labarai a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata.

A cewar ta, babu wani Bankin UBA a Afirka da bai tava samun asara ko faɗuwa ba sai dai riba da suke ta jawowa. Kuma suna cigaba da samarwa.

A farkon wannan shekarar ne dai aka naɗa Abiola Bawuah, ‘yar asalin ƙasar Gana a matsayin shugabar rukunan bankunan UBA a Afirka. Kuma ta kasance mace ta farko da tava hawa kan wannan muƙamin. Wannan naɗi nata ya nuna yadda bankin yake da burin ganin ya yi adalci a naɗe-naɗensa.

Yanzu suna da daraktoci 8 mata a ƙarƙashin rukunin bankunan. Kuma a baya ma ta kasance shugabar zartarwa a bankin UBA na Ghana. Bayan nan kuma ta riƙe muƙamin shugabar zartarwa ta shiyya.

Bankin UBA dai yana harkokinsa ne a ƙasashen Afirka guda 20, da Ingila, da Amurka, Faransa, da Dubai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *