Gwamnan Zamfara ya musanta bayyana kadara N9trn

Daga WAKILINMU

Gwamnan Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya musanta bayyana kadarori na Naira tiriliyan tara da aka ce ya yi kamar yadda aka yaɗa.

Gwamnan ya musanta hakan ne ciki sanarwar manema labarai da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a mai ɗauke da sa-hannun hadimin Gwamnan kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sulaiman Bala Idris.

Gwamnan ya bayyana rahoton a matsayin ƙage da aka shirya domin kawar da hankalin sabuwar gwamnati daga yunƙurinta na ceto Zamfara.

Ya ƙara da cewa, waɗanda suka faɗi zaɓe ne suka yaɗa ƙarairayin, kamar yadda suka yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Sanarwar ta ce sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta samar da natsuwar da ake buƙata a cikin harkokin mulki a jihar domin sauke nauyin da ke kan ta.

A cewar sanarwar, “Ba za a ɗauke mana hankali da irin waɗannan labaran na ƙarya a sfaukan sada zumunta ba, domin gwamnatinmu ta ƙuduri aniya kuma ta mayar da hankali kan kudirinta na magance matsalar tsaro da ilimi da samar da ruwan sha da inganta kiwon lafiya da noma da sauran ƙalubalen tattalin arziki da suka addabi jihar.

“Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyi da ayyukan da gwamna ya yi alƙawrin gudanarwa.”