Nasarori da ƙalubalen da Ma’aikatar Jinƙai ta fuskanta a saƙon Minista Sadiya na bankwana 

A wannan jawabi, za mu ji irin nasarorin da ma’aikatar jinƙai da kiyaye haɗurra (FMHADMSD) a ƙarƙashin Ministarta ta farko, Hajiya Sadiya Umar Farouq, a yayin da take bankwana da ma’aikatar. 

A lokacin da shugaba Muhammad Buhari ya ƙirƙiri ma’aikatar jinƙai a ranar  21 ga Agusta, 2019, manufar ƙirƙirar tata a bayyane take wato, kawo ɗauki na jinƙai don ceto waxanda ibtila’i ya ritsa da su, talakawa, da kuma tsamo miliyoyin ‘yan Nijeriya daga matsanancin talauci.  

Shugaba Buhari ya zavi Sadiya Umar Farouq a matsayin ministar hukumar ta farko saboda irin rawar da ta taka a baya a matsayin kwamishiniyar gwamnatin Tarayya, da kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da masu ƙaura da mutanen da suka vace (NCFRMI). Kuma Sadiya Umar Farouq, ta yi matuƙar ƙoƙari wajen tafiyar da harkokin Ma’aikatar duk da irin ƙalubalen da ke tattare da shi. 

A ranar 29 ga Mayun 2023, Shugaba Muhammadu Buhari yake barin gadon mulki ya miƙa shi ga sabon shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ita ma kuma Sadiya Farouq a ranar take bankwana da nata muƙamin kamar yadda kundin mulkin Nijeriya ya tsara na rushe majalisar duk wani mai barin gado, yayin da sabuwar gwamnati za ta kafa tata majalisar zartarwar. 

A dunƙule, abubuwan da Ma’aikatar jinƙai ta cimma a cikin shekaru uku da Hajiya Sadiya take jan ragamarta na tsahon shekaru 3 sun haɗa da, fitar da ‘yan Nijeriya guda miliyan 100 daga talauci ta shirin samar da walwalar al’umma (NSIP), wanda ya haxa da ciyarwar ‘yan makaranta (NHGSFP), samar da aikin-yi (N-Power), da shirin CCT da shirin GEEP), da sauran taimakon al’umma. 

Ayyukan kafa tarihi a jihar Zamfara
Ta wakilci shugaba Buhari a ranar 22 ga watan Mayu, wajen qaddamar da rukunin gidaje a yankin Kuraje da ke ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara. 

Hakazalika, Sadiya Umar Farouq ta ƙaddamar da ayyuka a Makarantar ‘yanmata ta Tarayya (FGGC), Gusau, da asibitin sha-ka-tafi a unguwar Dallatu in a ƙaramar hukumar Gusau, da sauransu 

Ma’aikata jinƙai da GAIN sun sanya hannu a yarjejeniyar fahimta a kan samar da lafiyayyen abinci:

A ranar 22 ga watan Mayu, hukumar jinƙai, FMHADMSD da ƙungiyar samar da lafiayyayen abinci ta duniya (GAIN) suka sanya hannu a takardar fahimtar juna don ciyar da makarantu. 

Yan Nijeriya sama da miliyan 15 sun mori ayyukan jinƙai:

A yayin da take jawabi, ministar jinƙai ta bayyana cewa, fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 15 ne suka amfana da ayyukan jinƙai daga hukumar ta jinƙai. Wato ta hanyar shirin NSIP, iyalai da dama sun yi katarin fita daga ƙangin talauci a ƙasar nan. 

Ta ƙara da cewa, shirin NSIP ya samar da tallafin da jinƙai ga miliyoyin ‘yan Nijeriya. Kamar shirin samar da abin yi, N-Power, shirin ciyar da ‘yan makaranta, shirin CCT da na GEEP. Gwamnatin tarayya ce ta ƙirƙiro da wannan shirin don tallafa wa ‘yan Nijeriya a faɗin jihohi 36 da birnin tarayyar Abuja. 

Ƙalubalan da maaikatar ta fuskanta:

Babban ƙalubalen da ma’aikatar take fuskanta shi ne yadda take buƙatar qara ƙoƙari wajen tsamo ‘yan Nijeriya daga Talauci. Amma har yanzu abin ya gaza ya kai yadda ake buqata. Domin alƙalumma sun nuna ‘yan Nijeriya sun kai miliyan 200 waɗanda har yanzu suke cikin tsagwaron talauci da waɗannan aikace-aikacen ba su riske su ba. 

Duk da irin dubban nasarorin da ministar da ta bar gadon ta samu a zangon mulkinta, ministar tana fusknatar wasu ƙalubalai. Kuma har yanzu suna nan. 

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, Hajiya Safiya Farouq ta yi iyakacin ƙoƙarinta wajen saita ma’aikatar amma ƙalubalen sun sha mata kai tare da sauran wasu dalilan da suka hada da siyasar cikin gida.   

A cewarsa, tun daga ranar da aka naɗa ta a matsayin minista take ta kai-komo don ganin ta yi abinda ya dace na tsamo al’umma daga talauci. Sai dai kuma abubuwa sun sha mata kai. Domin ma’aikatar ta kasance ma fi muhimmanci a gwamnatin Buhari gabaɗaya.

Sannan a cewar sa ga kuma jinkirin sakin kuɗaɗe daga ma’aikatar kuɗi don biyan  NSIP, NHGSFP da sauransu. Amma wannan bai sa ta yi rigima da kowa ba, a cewar majiyar. 

Haka a cewar majiyar, an yi amfani da siyasar cikin gida wajen daƙile mafiya yawa daga tsare-tsaren da ta niyyar samarwa. 

Kuma a cewar majiyar, ko ma waye zai gaji kujerar tata, ba zai tava kai wa kamar ta ba domin irin ƙure dukkan ƙoƙarinta da take yi wajen tafiyar da maaikatar. 

“Sam ba na jin ta akan duk wani muƙami da za ta samu a nan gaba. Ko da a ƙasar waje ne za ta iya riqe muƙamin yadda ya kamata.”