Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare ga nakasassu a jihar.

Gwamnati ta ce nakasassu za su ci gajiyar shirin gwamnatin jihar na bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare muddin sun mallaki abubuwan da ake buƙata.

Kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

A cewar Kwamishinan, “Yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tabbatar da adalci da samun daidaiton samun ilimi ga kowane ɗan jihar, daidai da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa.”

“Tabbas za mu bada tallafin karatu ga waɗanda ke da digiri na farko da na biyu, gami da nakasassu, don ƙarfafa su su zama ‘yan ƙasa masu fa’ida da rayuwa mai ma’ana.”

Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga jami’an ƙungiyar Mercy Corps da Coalition of Disabled Self Advocacy Network Group, wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da suka ziyarce shi a ofishinsa.

Ya ce, “Gwamnati za ta kuma duba yiwuwar kafa makarantun da za su haɗa da su a sassan jihar, kamar yadda kuma za a yi la’akari da damar da za a samar da kayayyakin aiki a makarantun gwamnati da ake da su.

“Wannan shi ne don tabbatar da cewa an aiwatar da nakasassu a cikin tsare-tsaren ci gaban mu.”

Ya jaddada cewa, a wani vangare na ƙudirin tallafawa nakasassu, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta ba su fom ɗin rajistar NECO guda 150, inda ya buqaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan dama ta yadda za a samu ingantacciyar rayuwa.

Kwamishinan ya yi alƙawarin cewa, gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen haɗa kai da ƙungiyoyi masu zaman kansu don kyautata jin daɗin jama’a, inda ya buqaci abokan hulɗar ci gaba da su sanya hannu a cikin manufofin gwamnati da shirye-shiryen gwamnati, don tabbatar da sakamako mai ɗorewa.

Tun da farko, Nafisa Amadu Abubakar, Ko’odinetan tsare-tsare da shawarwari, Mercy Corps da wasu wakilan nakasassu, sun buƙaci gwamnatin jihar da ta tallafa wa ƙungiyar domin gudanar da shirin samar da zaman lafiya a jihar, tare da tabbatar da cewa ba a bar nakasassu a cikin jihar ba, tsare-tsaren raya ƙasa na gwamnati.

A wani labarin kuma, Doguwa ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta haɗa kai da abokan hulɗar ci gaba, domin magance muhimman buƙatu na ilimi a jihar, musamman a fannin bunƙasa sana’ar malanta, ilimin ‘ya’ya mata, ilmin yara marasa galihu, da samun ilimin zamani.