Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin Bikin Easter

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma’a, 2 da Litinin 5 ga watan Afrilu, 2021 a matsayin ranakun hutun gama-gari albarkacin Bikin Easter na bana.

Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola ne ya sanar da haka a madadin Gwamnatin Tarayya a Abuja. Tare da yin kira ga ɗaukacin al’ummar Kirista da su rungumi ɗabi’ar zaman lafiya, son juna da yafiya kamar yadda Annabi Isa (AS) ya karantar.

Haka nan, Ministan ya buƙaci Kirista da su yi amfani da wannan dama ta Bikin Easter wajen yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya ga Nijeriya da kuma samun cigaba mai ɗorewa.

Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ga Ministan, Mohammed Manga, ta nuna Aregbesola ya bada tabbacin Gwamnatin Tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙarin da take yi na ci gaba da yaƙi da matsalar satar mutane, ta’addanci, fashin daji da dangoginsu da suka addabi sassan ƙasa.

Ya ce, “Sha’anin tsaro abu ne da ya shafi kowa, don haka ina kira ga ‘yan ƙasa da baƙi kowa ya zama mai kishin ƙasa tare da bada haɗin kai ga hukumomi da jami’an tsaro wajen ci gagaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.”

Baya ga fatan alheri ga waɗanda bikin Easter ya shafa, Minista Aregbesola ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su mara wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari baya don cika burinta na neman kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.