Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Spread the love

Daga UMAR M. GOMBE

‘Yanwasa da jami’an Ƙungiyar Ƙwallon Kafa ta Sunshine Stars a Jihar Ondo, sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira da rashin kulawa daga ɓangaren Gwamnatin Jihar.

Zanga-zangar wadda aka gudanar a birnin Akure ta yi sanadiyar haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci a yankin.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga babban filin wasannin motsa jiki zuwa fadar gwamnatin jihar ɗauke da kwalaye masu dauke da saƙonni daban-daban don nuna damuwarsu.

Waɗanda lamarin ya shafa sun ce ba su samu albashinsu ba na tsawon wata shida haɗa da sauran ihsanin da akan ba su na buga wasanni.

Haka nan, masu zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin Kaftin Abe Sunday, sun tafi har bakin ofishin gwamnan jihar da ke Akure don neman a saurari kukansu.

Sun roƙi gwamnatin jihar da ta taimaka ta biya musu buƙatunsu saboda a cewarsu, hakan na maida su baya a harkokinsu.

Maitaimakin Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, shi ne wanda ya karɓe su, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta share musu hawayensu.

By Editor