Gwamnati ta gurfanar da Tukur Mamu

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da tsohon mai shiga tsakani wajen tattaunawa da ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, kan zargin laifuka 10 da suka haɗa da taimaka wa ‘yan ta’adda da sauransu.

A ranar Laraba Ofishin Babban Lauyan Ƙasa (AGF) ya gurfanar da Mamu a madadin Gwamnatin Tarayya a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewar, a ranar 13 ga Satumban 2022 wata kotu ƙarƙarshin jagorancin Alƙali Nkeonye Maha, ta bai wa hukumar tsaro ta DSS damar tsare Mamu na kwana 60 domin ba ta damar kammala bincikenta a kan wanda ake zargin.

Mamu shi ne wanda ya jagoranci tattaunawa da ‘yan ta’adda wanda a sanadiyar haka aka sako fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja-Kaduna a Maris, 2022.