Tukur Mamu ya ƙi amsa tuhuma

Daga SANI AHMAD GIWA

Tsohon mai shiga tsakani wajen tattaunawa da ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, ya ƙi amsa tuhumar laifuka 10 da Gwamnatin Tarayya ke zarginsa da aikatawa.

A ranar Laraba ofishin Babban Lauyan Nijeriya ya gurfanar da Mamu a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin taimaka wa ‘yan ta’adda.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, Mai Shari’a Nkeonye Maha na wata kotun tarayya a ranar 13 ga watan Satumba, 2022, ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, izinin tsare tsohon ɗan mai sasanci tsakanin ‘yan ta’addan na tsawon kwanaki 60 domin ta kammala bincike kan Tukur Mamu, wanda ya jagoranci tattaunawar da ‘yan ta’adda domin sako fasinjojin jirgin qasa daga Abuja zuwa Kaduna da aka yi garkuwa da su a watan Maris xin 2022.

Darakta mai shigar da qara na gwamnatin tarayya, Mista M.B. Abubakar shi ne ya sanya hanya a takardar tuhume-tuhumen.

Daga tuhume-tuhimen da ake yi wa Mamu har da karɓar kuɗin fansa Dala 120,000.00 a madadin Boko Haram daga hannun ‘yan uwan fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna.

Laifin da Gwamnatin Tarayya ta ce ya saɓa wa Sashe na 21 (3) (a) dokar haramcin ta’addanci na Dokar 2022.