Gwamnati ta sanya ido ga jagororin zanga-zangar yunwa

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta sanya ido kan jerin sunayen masu jagorancin zanga-zangar yunwa da ke gudana a faɗin ƙasar.

Hakan ya bayyana ne daga bakin shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya, Kemi Nandap bayan fitowa daga tattaunawar tsaro da shugaban ƙasa.

Nandap wadda ba ta bayyana sunayen waɗanda a ka sanya sunayen su a jerin waɗanda a ke dako, tace ta mafi yawansu ba su zaune a Nijeriya, suna zaune a ƙasashen ƙetare.

Ta cigaba da bayyana cewa jami’an hukumar sun ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a iyakokin ƙasa da sama domin gudun shigowar agaji daga wajen ƙasar.

By ukarofi