Kamala Harris ta zaɓi ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa a zaɓen Amurka

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka kuma ƴar takarar kujerar shugabancin ƙasar, Kamala Harris ta sanar da gwamnan jihar Minnesota, Tim Walz a matsayin abokin tafiyarta a cigaba da shirye-shiryen zaɓen ƙasar.

Hakan na zuwa sakamakon karawa da za ta yi da tsohon shugaban ƙasar, Donald Trump a zaɓen da ke tafe a watan Nuwamba, 2024.

Walz ya zo da tsarin shiga karkara kamfe a sassan ƙasar ga jam’iyyar Democrat da karɓar tsare-tsaren ɓangarori daban-daban da kuma inganta ɓangaren kula da ma’aikata.

By Babaji