Gwamnatin Kano ta bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin ficewa daga fadar Nasarawa


Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika wa saukakken Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero takardar ficewa daga fadar Nasarawa inda nan ne Sarkin ya ke zama tun bayan da aka sauke shi.

Gwamnan ya yi hakan ne, yana mai cewa za su yi wasu gyare-gyare ne a fadar inda ya ce “bai dace Aminu Ado ya cigaba da zama a fadar ba” la’akari da rikicin Masarautar Jihar da ke cigaba da aukuwa.

A ranar Asabar da ta gabata ne, gwamnan ya sa hanu a kan kuɗi da adadin ya kai kusan kimanin naira miliyan 100 kan gyaran da za a yi wa fadar, inda ya ce akwai buƙatar Sarki Aminu Ado ya fice daga nan, domin gujewa wulaƙanci da tozarci.

Leave a Reply