Gwamnatin Sakkwato za ta maida yara 132,000 makaranta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF da gwamnatin jihar Sakkwato sun rattava hannu kan wata yarjejeniya, da nufin mayar da yara da ‘yan mata 132,000 zuwa makaranta.

Da ta ke zantawa da manema labarai bayan sanya hannu kan takardar a ranar Laraba, A’ishatu Ɗantsoho, babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin mata da ƙananan yara, ta ce shirin zai shafi ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Ɗantsoho ta ce haɗin gwiwar ya ƙunshi ɓangarori shida, sannan kuma an zaɓo ƙananan hukumomi takwas domin gudanar da shirin na gwaji don ɗaukar nauyin yara mata da ba su zuwa makaranta aƙalla dubu 5,000 a matakin farko.

Babbar Sakatariyar ta ce yayin da ma’aikatar za ta gudanar da shirin maida yara mata, hukumar kula da ilimin Larabci da Islamiyya za ta haɗa yaran Almajirai cikin ilimin boko.

A cewarta, za a mayar da yara da ‘yan matan da ba su kai shekarun makaranta zuwa tsarin karatu ba tare da tallafin ma’aikatar ilimi na farko da sakandare, da hukumar ilimin matakin farko ta jiha.

A nasa ɓangaren, Mustapha Ɗanjuma, mataimakin jami’in kula da ƙananan yara na UNICEF, ya ce yarjejeniyar mabuɗi ce ta samun ci gaba ta fuskar kare yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *