Real Madrid ta fasa sayen Mbappe – Ancelotti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce, ba zai sayi ɗan wasan gaba Kylian Mbappe daga Paris St-Germain a bana ba.

Mbappe, ɗan shekara 24 ya zuwa yanzu ya ƙi rattaba hannu a kan kwantiragi da PSG, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗin cewa zai koma ƙungiyar ta La Liga.

Ana tunanin cewa PSG a shirye take ta sayar da kyaftin ɗin na Faransa, maimakon yin kasadar rasa shi kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a shekara mai zuwa.

Da aka tambaye shi game da yarjejeniyar Mbappe, Ancelotti ya ce “A’a, na yanke hukunci kashi 100.”

Mbappe ya shafe tsawon lokaci yana atisaye, ba tare da ‘yan wasan PSG ba a wannan wata sakamakon taƙaddamar kwantiraginsa, amma ya dawo bayan tattaunawa da mahukuntan ungiyar.

An ajiye shi a wasan farko da kulob ɗin ya buga da Lorient, amma ya zura ƙwallo a raga bayan ya shigo daga baya a wasan da PSG ta tashi 1-1 da Toulouse a makon jiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *