Yadda rufe iyaka ya shafi rayuwarmu, cewar al’ummar iyakar Nijeriya da Nijar

Daga Jamil Gulma a Kebbi

Babu shakka rufe kan iyakokin da Jamhuriyar Nijar ta yi da Nijeriya ya ƙara rura wuta wajen sanya al’umma a cikin damuwa baya ga irin halin da ake ciki na matsin da rayuwa ta shiga na tsadar rayuwa da rashin abinci, musamman ga ’yan kasuwa da ke kai-komo tsakanin ƙasashen biyu.

Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Kebbi ya zagaya waxansu daga garuruwa da ke kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar kuma ya zanta da waɗansu mazauna yankunan.

Malam Salmanu Abubakar Dole-kaina wani ɗan kasuwa ne da ke sana’ar dabbobi a garin Dole-kaina, wanda ke kusa iyaka da ƙasashen Nijar da Benin, ya bayyana cewa, wannan rufe iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ya ƙara wa kaya tsada saboda kafin rufe boda ba su samun wahalar shiga Ƙasar Nijar, amma yanzu sai sun shiga Jamhuriyar Benin sannan su shiga Nijar, wanda sanadiyyar zagayen ya sa farashi ya tashi sosai sanadiyyar tsadar mai a jiragen ruwa da su ke amfani da su.

Haka zalika Malam Na’Allah wani direban jirgin ruwa da ke sufuri kan Kogin Neja da ya haxa Nijar da Benin, ya shaida wa wakilinmu cewa, yanzu sun sami ƙaruwar fasinja sanadiyyar rufe iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar savanin inda aka fito a baya kafin rufe iyaka sukan yi hada-hada ne ta waɗansu kwanaki da waɗansu kasuwanni ke ci kamar Lolo, Dole-kaina da Tsamiya saboda hanyar da suke sufuri ta ruwa ne da ya hada da Benin, yanzu ’yan kasuwa sun dawo ta hanyar Benin daga nan sai su shiga Nijar, haka zalika waɗanda ke zuwa Kwatano su ma su kan shiga ta nan.

A ɗaya ɓangaren kuma ya bayyana cewa, duk da ya ke waɗansu suna tsoron tafiya ta ruwa, amma a wajensu ba da ganin hatsarin duk ya ke jiragen suna ɗaukar kaya da yawa da suka da mutane da dabbobi da sauran kayan da ba haramtattu ba saboda yau da gobe ba su da a wata sana’a sai wannan.

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwa na Ƙaramar Hukumar Dandi a Jihar Kebbi, Malam Aliyu Zaki Kamba, ya bayyana rashin jin daɗinsu bisa ga yadda rayuwa ta kasance bayan rufe iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar saboda mafi yawancin al’ummar wannan yankin yankasuwa ne kuma kasuwancin nasu ya ta’allaƙa ne da wannan iyaka.

Saboda haka yanzu rayuwa ta shiga kunci saboda yanke hulɗar ya haifar da gurfanewar mutane da yawa har da masu masu babban jari ballantana ƙananan sana’o’i, domin idan ma ka buɗe shago ka ƙasa kayan babu masu saye.

Ya yi kira ga ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka da su nemi hanyar warware wannan matsalar cikin ruwan sanyi a buɗe iyaka, don mutane su koma su cigaba da harkokin kasuwancinsu duk da ya ke ko yanzu wannan abin ya yi wa mutane da yawa illa.

Malam Lauwali Garba Bachaka, Sakataren Ƙungiyar Direbobi Masu Sufuri A Ƙasashen Afrika, ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, yanzu haka akwai motoci maƙare da kaya; waɗansu a iyakoki yayin da waxansu kuma sun gaji da zaman ƙila-wa-ƙala sun haƙura sun dawo gida, ’yan kasuwa da su ke ɗauka zuwa fatauci a cikin ƙasashen Afirka suna nan zaune gida ba harkar yi yayin da su kuma direbobi sun sauya hanya a maimakon haka sun dawo da sufurinsu a cikin gida kafin a buɗe.

Ya ja hankalin direbobi da su guji biyar hanyar jeji, saboda komai zai iya faruwa, su cigaba da biyayya ga umarnin gwamnati kamar yadda suka saba.

Malam  Abdullahi  wani magidanci ne, da ya bayyana cewa, matansa biyu da yara bakwai, amma yanzu haka a halin da a ke ciki ba ya iya tuna ranar aka ɗora sanwa a gidansa sai dai ranar da ya sami sukuni a jiƙa garin kwaki a ci da ƙuli-ƙuli a sha ruwa a kwanta, domin maganar abincin rana ba ta ma  taso ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *