Ministocin Tinubu zafafa da sanyaya

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A ƙarshe dai kamar yadda kowa ya gani a labaru shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da ministocin sa 45 da Majalisar Dattawa ta tantance gabanin ta tafi hutu. In za a tuna har ma wataƙila daɗin kammala aikin tantancewar ya sa shugaban majalisar Godwill Akpabio ya ce ya tura ihsani ga dukkanin ’yan majalisar ɗari da tara don su more hutun.

A wani yanayi da a ka fahimci an ja hankalin Akpabio cewa ya na jawabi ne kai tsaye da a ke yaɗawa ta kafar talabijin, sai ya waske ko ya gyara zance da nuna ya tura addu’a ce ga akwatunan saƙonnin ’yan majalisar. Daga bisani bayanai daga wasu ’yan majalisar sun nuna Naira miliyan biyu ne a ka damƙawa kowanne daga cikin ’yan majalisar.

Wani daga ’yan majalisar da ba mamaki abun bai yi wa daɗi ba, ya fito ya ce irin wannan ihsani ba wani sabon abu ba ne wato ma’ana dama an saba tura ’yan majalisar saqon kuɗi kuma in ma an duba ai Naira miliyan biyu ba wasu kuɗi ne da su ka taka kara su ka karya ba in an duba dama ’yan majalisar masu hannu da shuni ne don ma ai akwai da yawa daga cikin su da tsoffin gwamnoni ne da su ka share wa’adi biyu kan kujera kafin tahowa majalisar.

Hakanan cikin ministocin akwai waɗanda su ka taɓa zama a majalisar a matsayin ’yan majalisar da bisa wata al’adar majalisar a kan ba su dama su wuce ba tare da wani ƙwaƙƙwaran bincike ba ko da kuwa su na da bunu a jikin su. Wasu kuma cikin ministocin sun shigo tantancewar da dogon turanci har ma da waɗanda a ka so tunzurawa su faɗi bayanai na bacin rai.

An ma ba da labarin akwai wacce ta zubar da hawaye da fakewa da cewa asalin ta talaka ce amma yau ta zama minista ko iyayen ta talakawa ne duk ba a tsawon shekaru an san iyayen irin waɗannan mutanen manyan mutane ne a kasa da tura ’ya’yan su, su lula karatu Turai ba wata babbar ɗawainiya ba ce.

A gaskiya ma abu ne mai kamar wuya a naɗa ɗan talakawan talak a matsayin minista a Nijeriya. Ko dai waɗanda a ke naɗawan boko baya diga a jikin su don kai wa ƙarshen Landan to z aka taras su na da wata alaƙa da manyan ’yan jari hujjar jihar su ko a bariki ko kuma na gaban goshin fadar shugaban ƙasa.

A taron rantsarwar a babban ɗakin taro na fadar Aso Rock, shugaban Tinubu ya hori ministocin su sauke abun da ya zayyana da alƙawuran kamfen. A nan dole a duba ko dukkan ministocin sun san alƙawuran da Tinubu ya ɗauka a lokacin kamfen?

Aqalla akwai wanda ma a ka samu da fitowa ƙarara ya sukar jam’iyyar APC a lokacin kamfen ɗin da nuna tamkar babbar annoba ce shiga irin wannan jam’iyyar amma a ka wayi gari ya shigo gwamnati har a na cewa ya tabbatar da nasarar alƙawuran kamfen. Hakanan an samu wani ma a cikin ministocin da a ka ga rubutun da ya yi ƙarara na sukar Tinubu da nuna ba daidai ne a yi mu’amala da mutane irin Tinubun ba.

Hakanan alamu sun nuna akwai waɗanda a gurguje a ka yafuto sunan su a ka jefa a jerin ministocin. Ai ga ma wani abu da ya faru a wajen tantancewa inda ɗaya daga waɗanda a ka tura sunayen su a ka janye alhali har ta shiga majalisar don tantancewa.

Kazalika an ji wasu daga ministocin sun fito don amsa tambayar kare kan su bayan sukar cewa an tura su ma’aikatun da ba su da wata ƙwarewa a lamuran aikin ma’aikatun.

Ga ma kuma yadda a ka karkare da batun tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasiru Elrufai wanda a ka nuna faifan bidiyon shugaba Tinubu na rokon sa ya yi aiki a gwamnatin sa har ma ya ce ba zai sauko daga dandamalin magana ba sai Elrufai ya yi alƙawari za su yi aiki tare. An ga Elrufa’in ya amince amma bayan tantancewa a majalisa sai a ka samu bayanin Elrufai bai tsallake tantancewar tsaro ba kuma duk da bayan ganawar sa da shugaba Tinubu bai sa an kammala tantance shi ba. Shin ko me ya faru a ka ga Elrufai ya fice ketare bayan nuna shi ya fi ƙarfin ya zama yaron kowa.

Mene ne ya sa Tinubu da ke roƙan su yi aiki tare ya goce da barin mutuncin Elrufai na walagigi a kafafen labaru? Wataran ma samu cikekken bayani saɓanin hasashe da kuma ra’ayoyi da ke fitowa daga masoya a gefe guda da kuma masu ƙin jinin Elrufai a ɗaya gefen.

Tinubu na nuna tun da sun rantse su ma sun zama kamar sun sa takalmi irin na sa ne wato sun zama a ɓangaren zartarwa ba batun bambancin siyasa, ƙabila ko rashin zama inuwar addini ɗaya.

Hakanan shugaban ya ce a yanzu ministocin sun zama masu aiki ne don wakiltar ƙasa baki ɗaya ba wani banhare ko ƙashin kan su ba. Ba na tsammanin dukkan kasa haka ta ke ɗaukar wannan lamari na minister cewa an naɗa su ne don yi wa kasa baki ɗaya aiki.

Tuni wasu jihohin na cewa ba a kyauta mu su ba don wa imma an ba su gurbin minista ɗaya a ka ba wa wasu biyu ko kuma an ba su qananan ministoci. Ba a rasa masu cewa an yi watsi da waɗanda su ka yi wa jam’iyya ko kamfen hidima a ka nada masu uwa a murhu.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Farouk BB Farouk ya ce ƙorafin wata jiha ta samu ƙarami ko babban minista ya saba wa tsarin dimokraɗiyya.

Wannan na zuwa daidai lokacin da qorafi ke fitowa na wasu jihohin ba su samu ma’aikatu masu tasiri ba ko maiko ba.

Dr. BB Farouk ya ce hurumin shugaban ƙasa ne ya naɗa wanda ya ga ya dace don zama minista da tura shi ma’aikatar da ya ke son ya yi ma sa wakilici a cikin ta.

A nan masanin ya nuna tamkar masu muhawarar ba sa la’akari da tsarin shugaba mai cikekken iko ne da Nijeriya ke aiki da shi kamar yadda ta ɗauko aron sa daga ƙasar Amurka.

Da ya juya kan samun ma’aikata mai tsoka, Dr. Farouk ya ce son samu duk wanda a ka naɗa ya yi wa ƙasa gaba ɗaya aiki ne kuma a baya an samu misalan da ke nuna ba lalle hakan ya kan kawo wata riba ba ce ”’Yar arewa ce ta sauka daga ma’aikatar kuɗi ina tushe na wani abu kwaya ɗaya da za ka ce arewa ta ƙaru, watakila in za ka gani z aka gani a gidan su ko a ƙauyen su ko a wani abu da ta ke so, haka za ka ce ai ilimi ɗan Arewa ne ya yi shekara takwas kafin wani ya zo ya hau yanzu to a ina za ka je ka samu wani abu da za ka ce ai an ingiza arewa a ilimin cikin shekara takwas ɗin ko don gidan su ko don wannan za ka iya gani amma ba za ka gani saboda al’ummar Arewa ba.”

A na sa martanin mai ba wa shugaban shawara kan siyasa Ibrahim Kabir Masari ya buƙaci ba wa sabuwar gwamnatin lokaci don ganin sauyin da su ka yi alƙawari.

A yanzu dai a na jiran sunan minista daga Kaduna da zai maye gurbin Nasiru Elrufai, sai sakamakon binciken tsaro ga Sanata Sani Abubakar Danladi daga Taraba da Stella Okotete daga Delta.

Har sabon minista Wike ya sha alwashin rushe gine-ginen da ba sa ƙa’ida a Abuja:

Da zarar rantsewa don fara aiki a matsayin ministan Abuja, tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike ya sha alwashin rushe duk ginin da ya saɓa wa ƙa’ida a Abuja.

Wike wanda kai tsaye ya shiga ofis a AREA 11 da ke kusa da fadar ta Aso Rock, ya ce zai yi aiki na ba sani ba sabo a jagorancin birnin.

Wike ya ce, zai dawo da birnin a ainihin yadda ya ke da kwace gidajen da a ka yi watsi da aikin ginin su musamman a manyan unguwannin Asokoro, Wuse 2 da Maitama. Kai tsaye ba a ji Wike ya kushe tsohuwar gwamnati ko tsohon ministan babban birnin wanda ya fi kowane minister daɗewa kan mukamin Muhammad Musa Bello da ba a saba gani ya na burga ko son yawan magana da manema labaru ba.

Kazalika rashin biyan kuɗin hayar ƙasa ma ka iya ja wa mai mallakar gini ko fili rasa kadararsa.

Da alamun mutane za su kai ruwa rana da ministan da a ke ganin na da ra’ayin taho mu gama.

Kammalawa;

Yanzu dai za a ce sai an gwada za a san na kwarai kuma lokaci zai nuna nagarta ko akasin ta ga sabbin ministocin na Tinubu. Kazalika za a samu ministocin da za su share tsawon gwamnati su na kan kujera irin yadda ya faru a gwamnatin Buhari ko za a riqa samun garambawul lokaci zuwa lokaci? Tun ba a je ko ina ba Tinubu ya sauyawa wasu ministocin na sa ma’aikatu kuma da ya ke ya na da hurumin yin hakan bai bayyana wani dalili ba.