Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Nijeriya a ranar Talatar da ta gabata ta bayar da cikakken ’yancin cin gashin kan harkokin kuɗi da na mulki ga ɗaukacin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Nijeriya ta hanyar yi wa sashe na 124 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar kwaskwarima.
Sashen ya tanadi samar wa ƙananan hukumomi cikakken ‘yanci ba tare da tsangwama daga gwamnatocin jihohi ba.
Gyaran dokar dai na ɗaya daga cikin wasu 22 da majalisar wakilai ta amince da ita a makon jiya kuma majalisar ta amince da ita a ranar Talata.
Ɓangarorin biyu sun ta hanyar kwamitin taro sun daidaita sassan gyare-gyare a cikin kundin tsarin mulkin da kowannensu ya aiwatar a watan jiya.
Bisa labarin da aka samu, Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da dukkan wasu sassa 23 da majalisun biyu suka yi wa kwaskwarima.
Sabuwar takardar da aka yi wa kwaskwarima, wadda za a aike wa majalisun dokokin Jihohi, domin amincewa, ta kuma amince da samar da ofishin Odita Janar na Ƙananan Hukumomi da kuma Hukumar Kula da Ayyukan Ƙananan Hukumomin Jihohi.
Sashen daidai ya share Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jiha (SIEC) daga kundin tsarin mulki ta haka ne ta bada ikon gudanar da zaɓukan kansiloli ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Sai dai ta ci gaba da riƙe kariyar da ke cikin kundin tsarin mulki ga Shugaban ƙasa da Gwamnoni ta hanyar yin gyare-gyaren da Majalisar Dattawa ta yi kan batun tare da yin watsi da sigar Majalisar wadda ta cire dokar kariya.
Majalisar ta kuma yi tanadin tsayawa takara mai zaman kanta a zaɓe mai zuwa a Nijeriya ta hanyar gyara sashi na 65 da 106 na kundin tsarin mulkin 1999.”
