Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A duk lokacin da ka ajiye aiki, abu na farko da ke faruwa da kai shi ne daina samun albashi daga wajen aikin da ka bari, amma ba haka abin yake ba ga ma’aikatan gwamnati da dama a Nijeriya.
Suna samun aiki a wasu wurare na daban, wani lokaci ma a ƙasashen waje kuma duk da haka suna ci gaba da karɓar albashi daga tsohon wajen aikin nasu.
Labarin irin wannan yanayi ya yi ƙamari ta yadda sai da ta kai ga a makon jiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike da kuma kawo ƙarshen wannan matsala.
Shugaban ƙasar ya ce; “Dole ne a tilasta wa duk masu hannu a wannan yaudara su dawo da duk kuɗin da suka wawura.”
Wani mutum da aka kira Sabitu Adams domin ɓoye asalin sunansa, bai ajiye aikin da yake yi a Nijeriya ba, a matsayin ƙaramin ma’aikacin gwamnati, domin haka shekara biyu kenan yana samun albashinsa kowanne wata, duk da cewa ya riga ya bar ƙasar.
Yanzu haka yana aiki ne a matsayin direban tasi a Birtaniya, amma ya shaida wa manema labarai cewa baya da wata fargabar yin asarar albashin da yake karɓa a Nijeriya, domin a cewarsa umarnin na Shugaba Tinubu ba komai ba ne illa barazanar da baki.
Adams ya ƙara da cewa, ba zai ji komai ba idan ya yi asarar albashinsa na Nijeriya wanda ya kai naira 150,000, wato dala 100 ko kuma fan 80 kenan, saboda a cewarsa yana samun fiye da hakan a matsayin direban tasi.
“Lokacin da na ji umarnin da shugaban ƙasar ya bayar, sai kawai na yi dariya saboda ina sane cewa abin da nake samu a nan ya zarce na gida Nijeriya. Ko kaɗan ban damu ba,” inji Adams mai shekara 36.
Amma mai ya hana shi shaida wa ma’aikatar da yake aiki a hukumance cewa ya daina aikin?
Adams ya ce; “Maganar gaskiya na ƙi sanar da su bana nan ne saboda ina tunanin idan zamana bai ɗore ba a nan, zan iya komawa in ci gaba da aikina a Nijeriya.”
KamarAdams, akwai ’yan Nijeriya fiye da miliyan uku da dubu ɗari shida da ke zaune a ƙasashen waje, waɗanda kuma sun shafe fiye da shekara biyu suna can, kamar yadda alƙalumma suka nuna.
Matasan ƙasar da dama ba su ganin cewa za su iya cimma burinsu na rayuwa a cikin ƙasar, wadda ke fama da matsalar taɓarɓarewar darajar naira, da kuma tsare-tsaren da Tinubu yake ɓullowa da su tun da ya zama shugaban ƙasa.
Ya zamo ɗabi’ar matasan ƙasar su nemi tsallakewa domin neman rayuwa mai inganci a ƙasashen waje, har ma sun yi wa irin wannan tafiya laƙabi da “japa”.
Kalmar Yarabancin ce da ke nufin ‘tsira’ ko ‘tsallakewa’.
Tinubu ya ce; “Na kaɗu da kalaman shugabar ma’aikatan gwamnati cewa akwai ma’aikatan da suka tsallake zuwa ƙasashen waje kuma duk da haka ana ci gaba da biyansu albashi kowanne wata”.
Shugaban ƙasar ya ce dole ne a ƙwato kuɗin da mutanen suka karɓa, kuma a gudanar da bincike domin ganowa da kuma hukunta duk masu hannu a ciki.
Ya ce, “Dole a hukunta dukkan shugabanni da masu kula da ma’aikatu da hukumomin da aka samu irin wannan badaƙala.”.
Kuma wannan na iya zama matsala ga Adams.
Direban tasin da ke aiki a Birtaniya ya shaida cewa yana cigaba da karɓar albashin nasa ne saboda taimakon wasu jami’ai a wajen aikinsa: “Ina da kyakkyawar alaƙa da maigidana a wajen aiki domin haka ya ba ni damar tafiya babu wata matsala”.
Mafi yawa dai ana ƙulla yarjejeniya ne tsakanin ma’aikacin da ke son tafiya da kuma shugabanninsa ko kuma masu lura da shi a wajen aiki, kuma ana raba albashin ne a tsakaninsu.
Amma ga Adams, abin ya zo cikin sauƙi kamar yadda ya ce; “Ban samu wata matsala ba saboda maigidana a wajen aiki ɗan uwana ne na jini.”
Ma’aikatan bogi babbar matsala ce a Nijeriya. Duk da matakai da ake ta ɗauka domin kawar da ita, ana ci gaba da samun dubban ma’aikatan na bogi da ake biya albashi, ko kuma wasu ke handame albashin nasu. Da alama kuma ba a ɗaukar wasu ƙwararan matakai a kai.
Amma wannan ne karon farko da aka fallasa cewa akwai mutane da yawa da suka bar ƙasar kuma ana ci gaba da biyansu albashi.
Auwal Yakasai, wanda ya taɓa tiƙe muƙamin Daraktan Kuɗi a Kano a shekarar 2021, ya shaida cewa, ya sha jin irin waɗanan matsaloli.
“Amma na samu labarai da yawa game da irin wannan yarjejeniya, inda mutum zai cigaba da karɓar albashi duk da cewa ya daina aikin ko kuma ya koma wani waje da aiki.”
Tun da ya hau mulki a bara, Tinubu ya sha alwashin rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.
A watan Janairu ya bayar da umarnin rage duk wata tawagar tafiyarsa, da ta sauran jami’an gwamnati da kashi 6o cikin dari, wannan kuma ya shafi tafiyar cikin gida da ta ƙasashen waje.
Sai dai kuma akwai masu ganin cewa gwamnatin Tinubun ta cika surutu babu cikawa.
Masu wannan ra’ayi sun kafa hujja da shirin gwamnatin na kashe miliyoyin dala wajen sayen jiragen sama ga Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettim.
Wani abin da suke kafa hujja da shi shi ne yadda a farkon watan nan Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon gidan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a birnin Abuja wanda aka kashe wa kuɗi har dala miliyan 13.6.
