Haɗin gwiwar Sin da Afrika a ɓangaren ababen more rayuwa a matsayin wanda zai bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen nahiyar

Daga CRI HAUSA

Wata ƙwararriya kan harkokin cinikayya da tattalin arziki ta ƙasar Ghana, Abena Oduro, ta ce haɗin gwiwa tsakanin nahiyar Afrika da ƙasar Sin a fannin ababen more rayuwa, za ta bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen nahiyar Afrika.

Abena Oduro, malama a sashen nazarin tattalin arziki na Jami’ar Ghana, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, raya ababen more rayuwa da suka shafi cinikayya, zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin ’yanci ta nahiyar Afrika.

Ta ce ababen more rayuwa da ake buƙata cikin gaggawa sun haɗa da layukan dogo da tituna da hanyoyin jiragen sama, waɗanda babu isassun da za su sauƙaƙa jigilar kayayyaki da hidimomi tsakanin wurare daban-daban, kamar yadda yarjejeniyar ciniki cikin ’yancin ke hasashe.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha