Almundahana: Kotu ta bada umarnin ƙwace kadarorin tsohon Gwamnan Zamfara, Yari

Daga BASHIR ISAH

A ranar Larabar da ta gabata wata Babbar Kotun Abuja, ta bada umarnin ƙwace wasu kadarorin tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, don miƙa wa Gwamnatin Tarayya.

Ƙwacewar ta wucin-gadi ce ta yadda a ƙarshe idan wanda lamarin ya shafa ya kasa gamsar da kotun, a nan ne kuma kotu za ta ƙwace kadarorin guda 10 na din-din-din.

Wannan na zuwa ne shekara guda bayan da wata Babbar Kotu ta yanke ma Yari makamancin wannan hukunci inda ta ƙwace maƙudan kuɗaɗe har miliyan N278.9 da aka alaƙanta su da tsohon gwamnan wanda ya mallaka ta haramtacciyar hanya.

Daga cikin kadarorin Yarin da kotun ta ƙwace wasunsu na Abuja ne, wasu a Kaduna da Zamfara da kuma Maryland a ƙasar Amurka.

Alƙali Obiora Egwuatu ya bada umarnin ƙwace kadarorin ne biyo bayan ƙudurin da lauyan hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ya shigar a kotu.

Alƙalin ya ce ya bada umarnin ƙwace kadarorin ne bayan gamsuwa da bayanai da kuma shaidun da lauyan ICPC ya gabatar wa kotu.

Ya ce wasu sassan dokoki da kuma dokar wawushe kuɗaɗe sun bai wa kotun hurumin bayar da umarnin ƙwato kadarorin Yari.

Ya ƙara da cewa bada umarnin ba zai hana a yi wa kowane ɓangare adalci ba a shari’ar, tare da buƙatar wallafa batun a wasu manyan jaridun ƙasa, kana ya buƙaci Yari ya rubuto takarda yana mai bayyana dalilan da za su hana ƙwace kadarorin nasa na din-din-din a miƙa wa Gwamnatin Tarayya.

Daga nan, Alƙali ya ɗage ci gaba da shri’ar zuwa ranar 28 ga Afrilu, inda za a ji shin Yari zai iya gamsar da kotu a kan kada ta ƙwace kadarorin nasa, idan kuwa ya gaza wajen gamsar da kotu, ya tabbata kotun za ta ƙwace kadarorin nasa kenan na din-din-din.