Matsalar damfara a yanar gizo

Babu makawa ga duk mai mu’amala da yanar gizo (wato internet) ko wayar salula ya san matakan kariya game yadda waɗansu ɓatagari ke baza tarko ta kowacce irin dama suka samu, don su damfari jama’a. Idan muka ce yanar gizo, to a nan mu na nufin ko wanne fanni na yanar gizo.

Shin kai ma’abocin shiga yanar gizo ne, don karanta labarai ko mai binciken ilmi ko ma’abocin kafofin sada zumunci da dai sauransu? Yau za mu kawo hanyoyin da su ka fi shahara wajen yin damfara a yanar gizo, kuma sanin su zai taimaka ma ka wajen tsallake tarkonsu, kuma har kai ma ka sanar da waɗansu.

Haƙiƙa a wannan zamani da mu ke ciki a iya cewa, yanar gizo ta zama larura a harkokin rayuwarmu na yau da kullum. A yau yanar gizo ta haifar da sauƙin gudanar da al’amura cikin. Misali; ta yanar gizo za a iya samun labarai da muhimman bayanai na kusan dukkan abin da ya shige maka duhu. Ga kafofin sada zumunta da ke bada damar ƙulla zumunci tsakanin yan uwa da abokan arziki, ta yadda za ku iya sanin lafiyar juna a kowanne lokaci ku ka so hakan kuma duk nisan da ke tsakanin ku. Sannan ta waɗannan kafofi akan sadu da waɗanda aka ɗebe tsammanin haɗuwa don kuwa ta yiwu an rabu ne tun lokacin da ba waya, kuma ba kafofin na sada zumunta.

Haka nan akwai hanyoyin bunƙasa kasuwanci, ga hanyoyin aikewa da kuɗi duk faɗin duniya cikin sauƙi, biyan kuɗaɗe irin na makaranta, wutar lantarki, ruwan famfo, tikitin jirgi da dai sauran al’amura masu kama da wannan. Ƙari a kan haka, akwai neman aiki, cike takardun makaranta, gudanar da jarrabawa… Kai abun da yawa, wai mutuwa ta je kasuwa, inji Bahaushe.

Sai dai abin takaicin shine, duk da waɗannan alfanu da yanar gizo ke da su ga al’umma, wasu ’yan damfara, maha’inta, masu son cin bulus, azzalumai sun fake da waɗannan ni’imomi su na damfarar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, maƙuden kuɗaɗe.

Mafi yawan mutane kan faɗa hannun waɗannan ’yan damfara a rashin sani, wasu kuwa saboda son banzarsu, don kuwa Bahaushe ya ce, idan ka ce za ka ba ni riga, to sai na duba ta wuyanka. Ƙwarai kuwa haka ne, domin misali shine, ya za ka ce za ka nuna min hanyar da zan samu Dala 1,000 kimanin Naira 300,000 a wuni, sannan ladan kuɗin da za ka nema a wajena bai taka kara ya karya ba? Idan gaskiya ne, kai ka bi waccan hanyar mana ka samu wancan kuɗin mai yawan. Ko ka fi so na da kanka ne?

Don haka mu ka ga zai yi kyau mu nusar tare da nunawa mai karatu musamman waɗanda ke faɗawa tarkon waɗannan azzalumai a rashin sani, mafi yawa daga ire-iren hanyoyin da su ke bi wajen damfarar mutane. Ba don komai ba sai don sanin hanyoyin da su ke bi zai taimaka ma ka kwarai da gaske ka tsallake duk irin tarkon da za su dana ma ka.

Sannan daga bisani za mu kawo hanyoyin kuvuta daga mugun nufinsu, amma da farko zai yi kyau mu jero hanyoyin da su ke bi don damfarar jama’a.

Ga wasu daga cikin hanyoyin da su ke bi nan:

 1. Tallar hanyar samun arziki da gaggawa.
  2.  Buƙatar ka biya su kuɗi.
  3.  A buƙaci ka saukar da (download) wata Manhaja (Software).
  4.  Samun kuɗi ko ribar da ta wuce hankali.
  5.  Bayanai masu tsoratarwa.
  6.  Neman aiki.
  7. Bayanai masu rikitarwa.
  8. Naci.

Hanyoyin kuvuta:
Tunda Blueprint Manhaja ta jerowa mai karatu hanyoyin da su kafi shahara wajen damfara a yanar gizo, yanzu za mu kawo hanyoyin kuɓuta a takaice.

1. Game da saƙon imel da su ke aikowa, mafita ita ce matuƙar ba kai ka buqaci wannan saƙo ba to ka rabu da shi.

Abu na farko, kar ka kuskura ka latsa inda suka buƙaci ka latsa.

Na biyu, ka dakatar da samun saƙon. A can kasan ko wanne imel akwai inda ake bada damar tsayar da samun saƙo matuƙar ba a buƙatarsa.
Na uku, ka goge saƙon, don kar ka manta watarana ka faɗa tarkonsu.

2. Game da tura kuɗi. Ka kiyayi tura kuɗi akan wani al’amari na yanar gizo ta hanyar ‘transfer’.

Guji tura lambobin katin amsar kuɗinka (ATM CARD).

Guji tura lambobin sirrinka na banki. Guji tura lambar shaidar bankinka ta BVN.

Idan wani al’amari ya shige ma duhu, tuntuvi sashen kula da abokan ciniki na bankinka don warware ma ka zare da abawa.

 1. Game da arzikin gaggawa. Ka yi watsi da irin wannan talla karma ka waiwaice shi, sannan ka guji sake ziyartar shafin don kuwa ’yan damfara ne.

4. Game da samun kuɗi a ƙanƙanin lokaci. Shi ma kamar na sama ne.

 1. Game da neman ka aika musu da kuɗi. Shi ma kamar na 3 ne.
 2. Game da naci kuwa sai mu ce ka yi uwar watsi da su, sannan ka latsa inda aka ce ‘Spam’ a akwatinka na imel bayan ka buɗe saƙon.
 3. Game da neman aiki. Ka nemi gamsasshen bayani dangane da shafin kafin ka je ga aikewa da takardunka.
 4. Game da samun kuɗi ko ribar da ta wuce hankali, kamar na uku na sama.
 5. Game da saukar da manhaja. Ka kiyayi saukar da manhaja daga duk ‘website’ da ba ka amince da shi ba.

A ƙarshe, muna kira ga masu karatu a duk lokacin da ka ci karo da wasu shirye-shirye a yanar gizo da kake shakku a kansu, yana da kyau ka tambayi wani da ka ke ganin ya fi ka ido a harkar yanar gizo. Idan hakan ba ta samu ba, to ka lura da sunan da suka bai wa shirin sai ka yi bincike akansa a yanar gizon. Abun nufi anan idan har ka gane sunan shirin sai ka rubuta shi a ‘Google’ don gano gaskiyar al’amarin.

Shi yadda tsarin yanar gizo ya ke, kamar yadda ake samun mutanen banza to kuma haka mutanen kirki na da yawa don haka za su baka bayani dalla-dalla game da wannan shirin ko ‘website’ ɗin. Wani ma za ka tarar an damfare shi ne a wannan Site ɗin sai ya yi rubutu don ya faɗakar da waɗansu.

Blueprint Manhaja na kira ga hukumomin Nijeriya da su gaggata kawo ƙarshen irin wannan damfare-damfare, ko dai ya yanar gizo ko kuma ta sauran hanyoyi da ke faruwa a cikin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *