Na tuna Magu, na tuna Kyari

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk aikin da mutum ya ke yi, ya yi addu’ar gama wa lafiya. Ba lallai tuƙin mota ko shiga ramukan haƙo ma’adinai ne ke da hatsari kaɗai ba, duk wata hidima ko fagen neman abun masarufi yana da irin na sa sammatsin, komai ka iya faruwa. Idan za a cewa mai aikin tuƙa babur ‘Allah ya kiyaye hanya da matsalar ƙarfe’ ya dace shi ma telan da ke ɗinki a ƙofar gida a ce ma sa ‘Allah kiyaye tsautsayi ya sa a tashi lafiya.’ Wannan tsari na da muhimmanci a sanya addu’a a duk abun da a ke gudanarwa na yau da kullum.

Ɗan adam tara ya ke bai kai goma ba, in mutum ya aikata wani aiki bisa kuskure ba za a yi mamaki ba sai a yi ma sa uzuri. Kuma hakan na iya faruwa ma da gangan, wato mutum ya aikata wani aiki da bai dace ba bisa ganganci don wasu daga mutane ba a rasa su da nau’i na son zuciya da kan sa su zarmewa ko aikata wani aiki da bai dace da mutum mai amana ba.

Ga misalin mai kushe gwamnati da rashin adalci wanda ɗan ƙasa na da hurumin bayyana ra’ayin sa kan abun da ya ga an aikata ba daidai ba don hakan ya zama jan hankalin gyara kayan ka. Za ka samu nau’in wasu daga masu ganin laifin gwamnati ko ma ’yan uwansu, na da wata ɗabi’ar da ita ma zalunci ne. Tauye mudu a wajen auna hatsi babban zalunci ne.

Yin wuf mutum ya wuce jar danja a kan titi nau’in zalunci ne. Tsame nama a miya da ya dace a ragewa sauran mutane ka iya zama zalunci. Gulma, sata, ƙarya, annamimanci, sakarci da lalaci duk munanan ɗabi’u da mutane ba za su so a yi mu sub a, amma wasun su in sun yi ba sa son a nuna mu su laifin su ko a hukunta su.

Zuwa yanzu ba za mu iya cewa tsohon shugaban rundunar matakin gaggawa na sufeton ’yan sanda DCP Abba Kyari ya aikata laifi a kira shi da mai laifi ba sai kwamitin bincike na shari’a ko kotu ta yanke hukuncin ƙarshe. Kazalika shi ma tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci Ibrahim Magu ba lalle ne mu kira shi a matsayin wanda ya zama mai laifi ba, bayan kammala bincike a kansa daga kwamitin shari’a na Jostis Ayo Salami.

Ma’ana ba mu ji rahoton me ya ke son a yi wa Magu ba bayan zayyana wasu abubuwa da ya nuna Magu ya yi ba daidai ba. Shin za a garzaya kotu ne ko kuma shikenan dakatar da shi daga muƙamin da naɗa sabon shugaba a hukumar Abdulrashid Bawa ya wadatar?

DCP Abba Kyari da CP Ibrahim Magu na mataki guda na waɗanda a ka dakatar daga aiki da mika cajin da a ke yi mu su ga kwamitin bincike. Duk jami’an biyu ‘yan sanda ne daga jihar Borno da ke matakin kwamishina a rundunar. Hakanan duk mutanen biyu musulmi ne. Hakanan duk mutanen biyu ba su da tsarin fargaba da hakan ba wai ya na nuna masu gaskiya kashi ɗari bisa ɗari ba ne.

Daga misalin abun da ya samu jami’an biyu da su ka yi suna ya isa ya sa sauran jami’ai su shafawa kansu ruwa wajen lura da hagu da dama su musamman in sun samu kan su a gidan gilashi. Sahihiyar magana ce da a ke cewa ba daidai ba ne wanda ya ke gidan gilashi ya zama ya na wasan jifa. Shi ma mai kaza a ƙugu ba ya jimirin as-as. A nan na sake tunawa da wata kamanceceniya tsakanin jami’an ’yan sandan biyu.

Bayan dakatar da su daga aiki an naɗa wasu da su ka maye gurbin su da hakan ke nuna ko za a janye dakatarwar, to ba dai lalle su koma kujerar da a ka kawar da su ba. A EFCC an naɗa Abdulrashid Bawa bayan kawar da Magu da riƙon ƙwarya na DCP Mohammed Umar; inda babban sufeton ’yan sanda ya naɗa Tunji Disu ya maye gurbin Abba Kyari bayan dakatar da shi.

Duniya kenan yau ka na da ban tsoro gobe ka wayi gari ka na jin tsoro. Yau ka na cewa a je a kamo wane gobe a ce a zo a kama ka. Yau a ce kai ne shugaban ofishi kaza gobe a wayi gari a ce kai ne tsohon shugaban hukumar kaza.

Kowa ya daɗe zai ga daɗau in kuma mutum bai daɗe ba fa me zai gani? Mu dai mu na fatan ganin alheri koyaushe da gamawa da aiki ko duniya lafiya. Ina tsammanin duk fatar da masu sanin yau da gobe na hannun Allah ne ke yi. In an damƙa wa mutum wani haƙƙi ko amana to ya tabbatar ya yi iya bakin ƙoƙarinsa ya tsare gaskiya da amana. Komai zai samu mutum ko ma ba jima ko ba daɗe matuƙar ya tsare gaskiya to gaskiyar za ta bayyana. Haka nan duk yadda a ka yi wa karya ado to fure za ta yi ba za ta haifar da wani sakamako mai ma’ana ba.

Na ziyarci Ibrahim Magu a lokacin da ya ke zaman dakatarwa na ga lafiyarsa ƙalau a fuska amma ba lalle lafiyar ƙalau a zuciya ba don in mai gaskiya ne zai yi ta zullumin ko gaskiyarsa za ta fidda shi? Hakanan na samu damar magana da DCP Kyari a lokacin da ya ke halin dakatarwa na ji ya na magana cikin natsuwa amma ba lalle a ce ba damuwa ta halin da ya tsinci kansa a ciki. Ba ni da hurumin yankewa kowa hukunci sai dai na yi tambaya ko na baiyana abun da na gani a zahiri.

Ana iya samun kuskure wajen yunƙurin tono abu na badini don ta kan yiwu mutum ya wuce hurumin abun da ya dace ya binciko har ma ta kai ga shiga haƙƙin wasu da ke alaƙa da wanda a ke yi wa binciken bayan fage. Ka ga binciken kan iya shafar yara ƙanana, abokai har ma kan iyaye.

Idan mun sake tunawa faɗar gwamnatin Nijeriya bayan kawar da Magu da nuna ya sava ƙa’idar aiki, ta baiyana cewa an zarge shi da mallakawa kan sa kayan da hukumar EFCC ke kwatowa daga ɓarayin biro. Shin an tabbatar da zargin nan ko kuwa a’a, sai mun jira mun gani. Aƙalla dai Magu na nan a gida ba hannun wata hukuma ba. Hakanan shi kuma DCP Kyari bayan turo binciken hukumar manyan laifuka ta Amurka FBI da ke nuna ya yi hulɗa da babban ɗan damfara Ramon Abbas, an dakatar da shi.

Yan a halin dakatarwar sai ga faifan bidiyo da ya ɓullo da sabon zargi kan Kyari daga hukumar yaqi da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA da ke nuna ya na da hannu kan wannan mummunar sana’a. Gabanin wani ya yi wuf ya ji martanin Kyari, sai rundunar ’yan sanda ta bayyana mika shi ga hukumar NDLEA don ɗaukar mataki na gaba. Jami’in ’yan sanda ya fita daga hannun rundunarsa da ke da duk kayan bincike zuwa rundunar yaƙi da miyagun ƙwayoyi na nuna girman zargi ko wani abu wanda zuwa yanzu mu mutanen gari ba mu fahimta ba kuma ba lalle aikin mu ba ne sai mun fahimta ko sai an fahimtar da mu.

Ibrahim Magu na nan a matsayin jami’in ’yan sanda kuma a bara ma saura kaɗan ya samu ƙarin girma zuwa mataimakin babban sufeton ’yan sanda, wato AIG, amma bayan baiyanar sunan sa sai kuma batun ya mutu murus. Me ya faru ne ya hana wannan mukami? Nan ma ina ganin ba sai mun matsa lamba mun gano ba, don ba mu da haƙƙin ƙara wa mutum girma ko rage ma sa girma.

Shi ma DCP Kyari na matsayin ɗan sanda a hannun jami’an NDLEA kuma an yayata cewa ya aikata kuskure wajen yin aikin ’yan sanda alhali ya na halin dakatarwa. Labarin da yanzu ya zo shi ne babban sufeton ’yan sanda Usman Baba Alkali ya rushe rundunar ɗaukin gaggawa IRT da Disu ya maye gurbin Kyari a aikin.

Ko rushe rundunar bai biyo bayan yadda a ka yi zanga-zangar neman rushe SARS ba, akwai alamun zanga-zanga a zuciyar babban sufeton kan rashin gamsuwa ko neman garambawul ga rundunar ta sa ta musamman. Rushe rundunar IRT ko SARS ba zai hana mutum ya fito kan titi ya gamu da ɗan sanda ba, da ya fito daga kowane aji na aikin ’yan sanda. Hatta ofishin da SARS su ka yi amfani da shi a Abuja ai bai san cewa an rushe ’yan SARS din ba don musamman yawan motocin da ke tsaye gaban ofishin ba su ragu ba kuma da alamun a na cigaba da gudanar da wasu ayyuka a ofishin. Ban san dai wace runduna ke aiki a wajen ba ko ba mamaki ’yan sanda na gama-gari ne ba zan iya yanke hukunci ba.

Haƙiƙa mu na buƙatar ganin gwamnati ko duk jami’an gwamnati na gudanar da aiki bisa dokokin da su ka ɗauki rantsuwa don kamanta gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *