Daga BASHIR ISAH
Babbar Kotun Kano karkashin jagorancin Alkali Usman Na’abba, ta yan ke wa wanda ya kitsa sacewa da kashe Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A ranar Alhamis kotun ta yanke wannan hukunci, inda ta ce dole Tanko ya bakunci lahira bayan kama shi da laifin kisa.
Tanko shi ne mai makarantar Nobel Kids Academy inda nan marigayiya Hanifa ke tafiya kafin cimma ajalinta.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 4 ga Disamban 2021 aka yi garkuwa da Hanifa a kan hanyarta ta komawa gida daga Islamiyya, inda daga bisani aka gano malaminta (Abdulmalik Tanko) ya kashe ta bayan kuma ya bukaci a biya kudin fansa har miliyan N6.
Kisan Hanifa ya daga hankalin al’umma matuka inda jama’a ta kowane ɓangare suka yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da adalci kan lamarin.
