An Gudanar da taron tattaunawa na wakilan jam’iyyu daban-daban

Daga CMG HAUSA

Kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin, ya gudanar da taron ƙara wa juna sani, kan yanayin tattalin arziki a halin yanzu da shirin raya tattalin arziki na watanni 6 na ƙarshen shekarar bana, inda aka saurari ra’ayoyi da shawarwari daga wakilan jam’iyyu daban daban na ƙasar Sin da shugaban ƙungiyar haɗin gwiwar masana’antu da cinikayya da kuma mutanen da ba sa cikin jam’iyya.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ne ya shugabanci taron, inda ya yi jawabin cewa, akwai sharuɗa masu kyau wajen bunƙasa ƙasar Sin, kana ana iya tinkarar matsalolin tattalin arziki da samun kyakkyawar makoma a wannan fanni.

Xi Jinping ya bayyana cewa, tun daga farkon shekarar bana, Sin ta gudanar da ayyukan yaƙi da cutar COVID-19 cikin nasara, da bunƙasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kuma an samu sabon ci gaba a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, ƙasar Sin baki daya ta yi namijin ƙoƙarin samun kyakkyawan sakamako.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a ci gaba da rigakafin annobar COVID-19, da daidaita tattalin arziki, da samun ci gaba bisa tsari na bai daya, da ƙarfafa farfaɗowar tattalin arziki, da ƙoƙarin cimma kyakkyawan sakamako.

Fassarawar Zainab