Daga AMINA YUSUF ALI
Gwamnatin jihar Ebonyi ta garƙame reshen Bankin GT na garin Abakaliki babban birnin jihar sakamakon rashin biyan haraji.
Gwamnatin ta bayyana cewa, ta kulle bankin ne sakamakon qin biyan haraji ga gwamnatin jihar Ebonyi. Kuma ta sha alwashin za ta cigaba da kulle shin har sai ya biya harajin da ake bin sa.
Tawagar masu ruwa da tsaki na ofishin hukumar tattara haraji ta jihar sun ziyarci bankin a safiyar ranar Talatar da ta wuce sannan suka ba da umarnin kulle shi a nan take.
Shugaban tawagar, Okoro Celestine, wanda shi ne shugaban hadaɗɗiyar hukumar tattara haraji ta jihar Ebonyi gabaɗaya, ya bayyana cewa, bankin ya yi buris da tunin da hukumar ta dinga yi masa a kan ya biya harajin da ake bin sa tun a watan Janairun shekarar nan ta 2022.
A cewar mista Celestine, wannan shi ne dalilin da ya sa hukumar ta nemi Sahalewar kotu wacce ta dogara da ita don ta garƙame bankin.
Kuma a cewar sa, ba wai wannan ne ziyarar farko da hukumar ta kawo ga bankin tana neman ya biya ɗimbin bashin harajin da ya taru a kansa ba. Tun 14 ga watan Janairu hukumar take ta zarya a bankin har zuwa yau. Kuma sun bi abin cikin tsari. Ba kawai zuwa suka yi suka kulle bankin ba, sai da suka je suka nemi izinin kotu sannan suka aiwatar.
“Sai da muka fara da yi musu gargaɗi na farko tun a watan Janairu, sannan kuma muka sake yi musu tuni daga bisani duk da haka suka yi buris. A Don haka ba mu da sauran zaɓi illa mu yi musu ƙarfi da yaji ta hanyar nemo umarnin kotu don a garƙame su”.
“Muna jin ya zama dole mu garƙame shi a yau. Kuma ba za mu taɓa buɗe shi ba, har sai sun yi biyayya. Ba yau muka fara wannan Bibiyar ba, tun daga Janairu zuwa yau, watanni bakwai kenan” Inji Mista Celestine.
Har zuwa lokacin da aka gama haɗa wannan rahoto, qoƙarin majiyarmu na zantawar da Manajan Bankin GT xin reshen Abakaliki ya ci tura.
