Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF, ta fitar da jerin ’yan wasa goma da ke takarar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2022.
Za a bayyana gwarzon bana a Rabar a Morocco ranar 21 ga watan Yulin 2022.
Cikin goman da Hukumar CAF ta sanar sun haɗa da mai riƙe da kyautar, Sadio Mane (Senegal da Bayern Munich) da wanda ya tava lashe kyautar Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City) da Mohamed Salah (Masar da Liverpool).
A bana ma dai lamarin bai zo wa Nijeriya da sa’a ba, inda babu ɗan wasan tawagar Super Eagles ko ɗaya da ya samu shiga jerin haziƙan ’yan wasan da Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirkar ta fitar ba.
Lokacin da aka fitar da jerin sunayen farko, ’yan wasan Super Eagles da suka haɗa da Moses Simon da Akinkunmi Amoo ne suka shiga jerin, amma daga bisani aka cire sunayensu bayan an yi tankaɗe da rairaya.
Sau biyar kacal ne a tarihi aka samu wani ɗan wasan Nijeriya ya lashe kyautar gwarzon CAF na shekara, inda Emmanuel Amuneke ya kasance na farko da ya taɓa lashewa a shekarar 1994, sannan Kanu Nwankwo ya lashe kyautar a shekarar 1996.
Bayan shekara ɗaya kuma Victor Ikpeba ya zama gwarzon ɗan wasan shekaara na CAF, kafin Kanu ya sake karɓe kambun bayan shekaru biyu.
Ga jerin ’yan wasan Afirka 10 da ke takarar gwarzon ɗan ƙwallon CAF na 2022:
- Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City).
- Karl Toko Ekambi (Kamaru da Olympique Lyonnais)
- Vincent Aboubacar (Kamaru da Al Nassr)
- Sebastien Haller ( Kwaddebuwa da Ajax)
- Mohamed Salah (Masar da Liverpool)
- Naby Keita (Guinea da Liverpool)
- Achraf Hakimi (Morocco da Paris Saint-Germain)
- Edouard Mendy (Senegal da Chelsea)
- Kalidou Koulibaly (Senegal da Napoli)
- Sadio Mane (Senegal da Bayern Munich).
