Hisbah za ta cafke Musulmin da ba sa azumi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi barazanar hukunta duk waɗanda aka kama su na aikata munanan ɗabi’u a wannan wata mai albarka na Ramadana, ciki har da ƙin yin azumin na watan Ramadana.

Hakan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Ibrahim Lawan, ya fitar ranar Alhamis a Kano, inda ya ce, Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Dakta Harun Ibn-Sina, ya bayyana cewa, waɗanda suke aikata munanan ɗabi’u a cikin wannan wata mai alfarma, za a yi maganin su.

“Wasu daga cikin matasan da ke cin abinci a bainar jama’a a lokacin azumi su ma ba za su tsira ba,” inji shi.

Malam Ibn-Sina ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa marayu da mabukata a wani yunƙuri na rage raɗaɗin da suke ciki.

Ya kuma bayyana cewa, Hisbah za ta tura jami’anta zuwa masallatai, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a cikin watan Ramadan.

Babban Kwamandan Hukumar, ya ce, “Rundunar Hisbah za ta ziyarci masallatai a lokutan buɗe-baki, tarawihi da tahajjud, domin kare masu ibada da dukiyoyinsu daga rashin kishin ƙasa.”

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Mai Alfarma Sarkin Musulmi,  Alhaji Sa’ad Muhammadu Abubakar na III, ya sanar da ganin watan Ramadan, inda aka tashi da shi jiya Alhamis.

Watan Ramadan dai wata ne na fifita ƙasƙantar da kai, inganta ibada da neman yardar Allah a wajen al’ummar Musulmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *